TA ADDANCIN SABUWA DA FASKARI

0

TA ADDANCIN SABUWA DA FASKARI

Muazu Hassan

@Taskar Labarai

Mahara masu dauke da miyagun makamai sun shiga garin Machika dake karamar hukumar Sabuwa a daren 30/8/2020 sun tafi da mutane hudu kamar yadda Jaridar Taskar Labarai ta tabbatar, mutanen sune Idris A Maikudi, Musa Bala Abubakar Shema da Amiru Badamasi.

A kuma daren wasu gungun mabarnatan suka je garin Mararrabar Kindo suka ce kar wanda ya fito da asuba sallah, sai sun kammala abin da ya kawo su, sun tafi.

Maharan sun rika bin shago-shago suna kwasar kayan abinci da na amfani, sannan suka fice garin ba tare da sun taba lafiyar kowa ba. Sannan jama’a suka fito daga cikin gidajen su, kamar yadda jaridar nan ta tabbatar.

See also  AN SAKO 'YAN BATSARI, BAYAN KWANAKI 66 A DAJI .

Maharan sun fada cewa, suna huce haushin su ne, akan jama’a daga matsin da suke sha daga wajen jami’an tsaro/na hare-hare akan sansanoninsu da toshe duk wata kafa ta madatsar su.

Taskar Labarai ta gano wadannan masu rike da makamai suna danyen aiki, suma sunyi noma a wasu yankunan Dandume, Faskari da Sabuwa, har gargadin mutane suke kar su kuskura su taba masu gonaki, Taskar Labarai ta tabbatar hatta mutanen yankunan sun san gonakin da wadannan ‘yan ta’adda ke nomawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here