WADANDA AKA SACE A KURFI SUNA ZAMFARA
Ahmad Mahmood
@Taskar Labarai
Matan nan da aka sace a garin Kurfi ta jihar Katsina suna a wani daji na cikin jihar Zamfara kamar yadda wata majiya ta tabbatar mana.
Maharan sun zo ne, daga Zamfara suka hadu da wasu masu basu labari yan asalin yankin.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa ana tafiya da matan cikin dare basu tsaya ko’ina da su ba, sai sansanin nasu da ke kusa da wata babbar karamar hukuma dake cikin jihar Zamfara.
Wata mata da maharan suka sako daga garin Kurfi ta tabbatar wa da jaridar Taskar Labarai cewa, Ita ma a wannan sansanin na jihar Zamfara aka tsare ta, har sai da ‘yan uwanta suka biya kudin fansa sannan suka sako ta. Inda suka kawo ta babban titi, a cikin Zamfara aka je aka dauko ta.
Ta tabbatar wa da Taskar Labarai cewa, ta na can aka kawo wadannan matan da aka dauko daga Kurfi aka hada su a waje daya.
Iyalan wadanda aka sace daga garin na kurfi sun tabbatar wa Taskar Labarai cewa, sun yi magana da maharan har aka yi tsadance akan naira miliyan hudu, daga baya suka amince akai naira miliyan biyu.
Iyalan suka ce, bayan sun tara kudin har naira miliyan biyu da kyar. Suka kai, sai ‘yan ta’addar suka ce, sai an ciko naira miliyan biyu ko su kashe matan.
Iyalan sun tabbatar wa da jaridar nan cewa, yanzu kokarin da suke tayi ke nan sake hada wata naira miliyan biyu, su kai don a sako matan nan.
Sun tabbatar ma da jaridar nan cewa inda suka kai biyan farko na kudin daji ne tsakanin Zamfara da Katsina, kuma wanda ya amshi kudin yace daga Zamfara yake.