Matar Gwamnan ta haddace Rabin Kur’ani

0

Daga Ibrahim Hamisu

Matar Gwamnan jihar Naija, Dr Amina Abubakar ta haddace rabin Kur’ani. A wata hira da Daily Trust ta ce a duk sati takan haddace shafi 1,

Tace takan dauki aya 3 ne daga Sallar Asubahi, wani lokacin ta dauki mintuna 30 wani lokacin kuma awa 1, ya danganta da yawan ayoyin. Tace idan ta dauka da Sallar Asuba to za tai ta maimai a cikin sallolinta na ranar har sai ta haddace, idan kuma bata hadda ce ba sai ta sake maimaitawa washe gari.

Ta kara da cewa domin ta rike haddar takan yi kokarin karanta Rabin Juz’i kullun kafin sallar Asuba sannan kuma takan rika maimaitasu cikin sallolin Nafila da take yi.
da aka tambayeta ya take yi wajen ayyukan yau da kullun,  tace idan ayyuka suka yi mata yawa takan maimaita karatun da ta haddace a baya.

Tace tana da malama dake mata karatun kuma sukan hadu duk karshen mako, amma idan ayyuka suka yi yawa basu hadu ba, sukan yi amfani da waya domin ta yi mata kari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here