HARI A KARAMAR HUKUMAR DAN MUSA
Mahmod hassan
@ taskar labarai
A daren jiya wasu mahara sun kai Hari a garin yan tara, sabon gari nasarawa ta karamar hukumar Dan Musa.jahar katsina
Maharan sun shigo garin da kamar karfe sha biyu da rabi na dare kamar yadda ganau suka tabbatar wa da taskar labarai.
Mutanen sun bar cikin garin suka koma wajen suka yi ma maharan kwantar bauna.barayin sun kwashi dabbobi da kayan abinci. Suna kan hanyarsu ta fita sai mutanen garin suka afka masu.
Inda aka fafata suka kwaci dabbobinsu da kayansu kamar yadda taskar labarai ta tabbatar.
Ganin Haka barayin suka tarwatse suka shiga daji.
A fafatawar an kashe daya daga cikin maharan.wani kuma daga cikin mutanen garin yayi Shahada.an kuma sari mutum daya da adda .tun cikin daren aka kai shi asibiti.kamar yadda ganau suka tabbatar wa da taskar labarai.
Za ayi Jana izar Wanda maharan suka kashe yanzu da safe.
________________________________________________
Taskar labarai ce kadai ke da wakilai da bangarorin da mahara ke matsamawa don kawo maku abin da ke faruwa da dumi duminsu.
Tana a bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta.duk sako a aiko ga 07043777779