Shu’aibu Ibrahim Gusau
Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara Hon Dr. Bello Mohammed MON (Matawalle Maradun) ya bayyana kudirin gwamnatin sa na kiyaye dukkan Zakka da wakafi da bin umarnin Musulunci.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya lokacin da ya karbi rahoton kwamitin da aka kafa domin binciken takaddamar da ta kunno kai tsakanin mambobin da ke Gudanar da hukumar.
Gwamna Matawalle ya ce dole ne a ba Zakka matsayin daya daga cikin shika-shikan Musulunci duk abin da ake so don kiyaye umarnin Musulunci a cikin al’ummar Musulmi.
Ya Kuma ci gaba da cewa, Hukumar Zakka na matsayin daya daga cikin muhimman bangarorin aiwatar da Shari’a wadanda suka taimaka matuka wajen rage wahalhalu a kan marasa karfi a jihar Zamfara ,wanda gwamnatinsa ba za ta yi sakaci da shi ba.
Malam Tukur Sani Jangebe kuma shugaban kwamitin binciken badakalar hukumar zakka da wakafi ta jihar zamfara ,da yake mika sakamakon binciken nasu, sun ba da shawarar da a gaggauta rusa mambobin kwamitin tare da nada sabbin mambobi wadanda ya nuna cewa ya kamata a koma fikihun Musulunci don manufar samar da hadadden kwamiti wanda zai ci gaba da bin manyan manufofin wannan gwamnatin.
Jangebe ya Kara da cewa kwamitin yana ba da shawarar , Gwamnati ,ta lura da bin ƙa’idoji da bin hanyoyin da suka dace.
Kwamitin ya wanke Daraktocin guda biyu wadanda aka dakatar tun farko saboda ba ta same su da karya ka’idojin kudi ba kamar yadda ake zargi.