Zamfara ta bude hedikwatar hukumar temeke- keniya ta lafiya

0

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Gwamnan jihar zamfara Hon Bello Mohammed Matawalle, ya bude hedkwatar Hukumar temakekeniya ta Lafiya a gusau babban birnin Jihar Zamfara (ZACHEMA) a yayin da ake kaddamar da shirye-shiryen yin rajistar, da bayyana ka’idojin aiki da fa’idodi don amfanin mazauna jihar.

A cikin jawabinsa a wurin bude ofishin ya bayyana cewa jajircewar da gwamnati ta yi na ganin an cimma wannan tsarin, ya ce sun yanke shawarar gina wannan babban hedikwatar ga ZACHEMA tare da samar da abubuwan da ake bukata don gudanar da ofisoshin yadda ya kamata sannan kuma sun tura ma’aikatan da ke aiki a hukumar tare da horar da su.

Ya Kara da cewa Kididdigar zamantakewar jama’a ta nuna cewa sama da kashi 74% na‘ yan Nijeriya na biyan kudin kiwon lafiya ta hanyar dan abin da suke samu, yace a wasu jihohin, daga 85-92% sun dogara ne da ƙididdiga daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

See also  Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Wata Karamar Hukuma A Jihar Taraba

Ya kuma ce gwamnatinsa ta yi kokari wanda ya hada da samar da motocin daukar marasa lafiya 23 ga cibiyoyin kula da lafiya a duk fadin jihar da kuma gina sabbin dakunan shan magani na mata da yara a dukkan kananan hukumomi 14 na jihar, ya ce yanzu haka muna gina Cibiyoyin Kula da Kiwon Lafiya a matakin farko 147 a duk yankunan karkarar jihar kan kudi sama da N2billion.

Ya bayyana cewa za a samar da kowane asibiti mai daukar gadaje 50 da motar daukar marasa lafiya don jigilar marasa lafiya zuwa asibiti daga wurare masu nisa da nufin rage wahalar kai marasa lafiya daga wuraren karkara zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na sakandare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here