BINCIKEN APC A KATSINA: ZIYARATA A OFISHIN APC

0

Suleman Chiroma

Ni ba Dan Katsina bane ina kula da shafin The Links News ne daga Kaduna, dan asalin Kaduna ne, kuma gidan sarauta, na kan zo Katsina don tattaunawa akan jaridun Taskar Labarai.

A ranar 26/7/2020 muka yi meeting akan bincike-binciken da muke, da lokacin da ya kamata a fitar da kowane, da kara tantance matsayin kowane.

A ranar aka fitar da takardu guda uku kowane za a kaima wadanda ake aiki akan su don a basu dama su bada nasu bayanin kamar yadda dokar aikin ta tanada.

Ni aka ba in kai ofishin APC, a ranar 28/7/2020, na je ofishin tun karfe goma na safe babu kowa na samu waje na zauna, har sha biyu babu kowa, na kira babban edita nace ga halin da ake ciki ya jaddada mani cewa dole in tabbatar da cewa na ba wani takardar nan ya amsa kuma an sa mani hannu.

Nan na zauna ina ta mamaki, wane irin ofishin jam’iyya ne wannan? Kuma na jam’iya mai mulki? Kuma shalkwatarta?

Nayi yawo a jihohi duk inda na je ofishin jam’iyyar matattara ce, wajen hutawa ta mutanen kirki ‘yan jam-iyya na gari amma a Katsina kamar anyi yaki ba ayi nasara ba.

Da yunwa ta ishe ni, naje neman abinci, ina dawowa kusan biyu na iske an bude ofishin na hau sama nayi ta sallama, sai dai sallama ta ta rika amsa kuwwa, kamar irin gidajen nan na finafinan ban tsoro, ba kowa kuma kamar anyi shekaru ba a shiga aka yi wani taro ba a cikin ofishin.

Hana karya naga kyankyasai suna shigi da fici ofishin shugaban na jiha, ga yanar gizo da datti ko’ina ga kura Allah ya taimaka ina da marfin rufe fuska, wanda na saba da shi a Kaduna.

Ina gab da fitowa mu ka yi arba da wani bera suna tsare da dan uwansa na kauce na basu wuri ina kallon ikon Allah.
Na sauko na samu wani wuri can na zauna, ina jiran in ga shigar mutum in bishi kafin nan na fara tambayar wai ina shugaban ne?

Aka ce mani ai tun da hukumar kwastam ta rufe kamfanin sayar da motocin shi wanda yake daura da shalkwata, ya bar zuwa ofishin, aka ce mani amma an kusa warware matsalar don hukumar ta kwastam ta sanya ma kamfanin kudi kuma ana rade radin wasu zababbu a majalisar kasa zasu hada kudin su biya mashi, an ce wai-wai-wai har sun fara asusun gidauniyar tallafawa don a bude masa kamfani, kaji dangata.

A magana da abokan hira ta na gano ashe shugaban ma na jiha asalin shi talakkan kasar da uwaye na ke mulki ne, cikin zuciya ta nace Allah ya sanya yau inga dan gida da Allah yayi ma arziki a Katsina, har waya na buga ma dangi cewa da gaske ne, wane a Katsina dan nan ne? Sai aka yi ta koro mani bayani.

An fada mani cewa, ai shugaban ya maida komai na jam’iyyar zuwa gidan shi ( daga baya na kai ziyara gidan inda naga ikon Allah, amma fa ban samu ganin shi shugaba ba. Gani da ido ya kaini kuma na gano).

Ina zaune na hango wani mutum zai hau saman benen na same shi na bashi takardar ya sa mani hannu na, na bar wajen.

Tun karfe Goma na safe sai uku da rabi na rana, na ga Dan Adam ya shiga ofishin na jam’iyya, na buga waya ga babban edita na shaida masa, yace inyi hakuri haka aikin ya gada in dai bincike zaka yi na hakika, kuma kana son ka baiwa kowa damar sa don kayi adalci.

Da muka dawo miting kusan duk wasikun da muka aika mun samu amsa, banda wadda na kai ofishin da talakkan kasa ta ke shugaban ta, wasu amsar da suka bada ya sanya. Babban edita yace a jingine binciken a kuma dakatar da rahoton. Misali akwai bincike akan babbar asibitin gwamnatin tarayya, dake Katsina, suma mun aika masu wasiku guda biyu, amsar da tazo mana babban edita yace a dakatar da shi kuma a jingine rahoton.

Wasu guda biyu babban editan yace a sake lalen binciken cikinsu har da yarjejeniyar da gwamnatin Katsina ta shiga da wani asibiti mai zaman kansa akan yin gwaji akan gano masu dauke da cutar covid19. A game da APC babban edita yace a sake aika masu da takardar tuni akan wasikar farko, kuma akayi ni aka sake ba na kaita, nan ma wani labarin ne daban.
________________________________________________
Taskar labarai na bisa yanar gizo akan shafin www.taskarlabarai.com da ‘yar uwarta ta Turanci mai suna The Links News akan www.thelinksnews.com. duk sako a aiko ga katsinaoffice@yahoo.com ko 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here