ALLAH YA JIKAN SARKIN MUSAWA MUHAMMADU GIDADO( 1943 _2020)

0

TA AZIYYA;

An haifi Muhammadu Gidado a ranar Lahadi 20 ga watan Yuni shkarar 1943. Ya yi karatunsa na Allo a hannun malaminsa marigayi Malam Iro mai Mazuru a cikin garin Musawa. Ya kuma halarci makarantar karamar firamare da ke Musawa a cikin Shekarar 1950 zuwa 1954, sannan ya halarci babbar makarantar Firamare da ke Kankia a cikin Shekarar 1955, daga nan sai aka maida shi Firamaren da ke Minna a Jihar Neja a shekarar 1956-1957.

Daga nan ya wuce karamar makarantar Sakandire da ke a garin Suleja 1958, da aka daukaka darajar makarantar zuwa babbar makaranta, sai ya cigaba da karatunsa a makarantar a shekarar 1963. Bayan ya kammala karatunsa sai ya ci jarabawar makarantar horon malamai da ke Bauchi domin ya samu shedar koyarwa mai daraja ta biyu (wato Grade II). Har ya fara shirin tafiya sai mahaifinsa Durbi Usman Liman ya ce “gara ya tafi kasar Ingila ya yi jarabawa samun shedar gama makarantar Sakandire G.C.E idan ya kammala sai ya shiga Jami’a”. Saboda haka, nan da nan aka sama masu takardun tallafin karatu na gwamnati zuwa kasashen waje da shi da kaninsa Dr Yusufu Bala Usman. Wanann ne ya basu damar shiga makarantar Enfield College of Techology dake a kasar Ingila inda ya fara karatun ilimin koyon kimmiyar yanayi da halittun ‘yan Adam. Ya kwashe tsawon shekaru biyu a kasar Ingila daga 1963 zuwa 1965, sai maganar sarauta ta taso wadda tasa dole ya bar karatunsa ya dawo gida domin ya gaji mahaifinsa.

Bayan nada shi sarauta ya dade ya na son ya koma ya cigaba da karatunsa, har ma a cikin shekara ta 1967 bayan an nada shi ya nemi ya shiga wata jami’a ta kasar Amurka mai suna Peace University to amma a lokacin sai Mahafinsa Durbi Usman Liman ya ki amincewa ya sa aka hana shi shedar izinin shiga kasar Amurka da dukkan wasu takardu da ya ke bukata. Daga karshe dai sai ya rungumi kaddara ya tsaya ya shiga harkokin Mulki gadan-gadan. Sai dai ko kadan bai yi nadamar abinda mahaifinsa ya dora shi a kai ba na sarautar hakimcin Musawa, saboda ya na matukar alfahari da irin gudummuwar da ya bada a fannin cigaban kasar Musawa baki dayanta.

Sarkin Musawa, Alhaji Muhammadu Gidado ya taka muhimmiyar rawa wurin kawo gagarumin cigaba ga al’ummar da ke kasar Musawa, da Matazu da Jikamshi baki daya. A bangaren ilimi, a zamanin da ya hau kan gadon Sarautar Musawa a tsakanin Shekarar 1965-1966, akwai makarantun firamare guda biyu kawai a garin Musawa da Matazu. Amma yanzu kusan kowane lungu da sako na kasar Musawa na gina makarantum Firamare da sakandire daban-daban.

A lokacin ya na wakili a kwamitin bunkasa ilimi na kasar Katsina da Daura. Ya yi kokarin ganin an gina makarantar sakandire a Musawa domim da an so gina makarantar a Dutsinma ne ya yi tsaye nemi taimakon Matawalle Musa Yar’adua da Iyan Katsina Alhaji Ibrahim Mashi wadanda suka tsaya suka tabatar da cewa an gina makarantar sakandire a Musawa. Sannan shi ne ya yi dalilin da ya sa aka kara gina manyan makarantun sakandire a garin Matazu da Jikamshi da Dangani da kuma Tabanni, sannan an sake gina wasu makarantun a nan cikin Musawa harma da makarantar al’umma mai zaman kanta mai suna Dandattijo da ke nan Musawa.

A bangaren lafiya, a zamaninsa ne aka gina asibitin garin Musawa da wuraren shan magani a dukkanin garuruwan Magaddai da wasu kauyukan dake kasar Musawa. Sannan a zamaninsa ne aka hada garin Musawa da lantariki sannan kuma aka gina mata babban Dam, kuma an samar da hanyar da ta taso daga Charanci zuwa Kafinsoli zuwa Matazu zuwa Musawa ta bulle zuwa Kurkujan, kuma wannan hanya ta kara bunkasa tattalin arzikin al’ummar kasar Musawa. Sannan ya yi kokarin ganin cewa, an bunkasa harkar noma sosai ta hanyar tabbatar da samun takin zamani da sauran abubuwan da za su kara bunkasa harkokim noma da bunkasar abinci a garin Musawa.

Bayan nada shi Sarkin Musawa, Alhaji Muhammadu Gidado ya yi aiyuka da dama domin cigaban kasa, shi ne shugaban masarutar karamar hukumar Musawa tun shekarar 1965 zuwa rasuwarsa. Ya yi wakili a hukumar mulkin karamar hukumar Dutsinma a shekarar 1970 zuwa 1974 da karamar hukumar Kankiya 1974 zuwa 1975 ya yi wakili a hukumar kula da ilimin jihohin Arewa ta tsakiya daga shekarar 1970 zuwa 1974.

Sarkin Musawa Muhammadu Gidado yayi wakili a hukumar adana kayan tarihi ta jihar Kaduna a shekarar 1974-1978. Sannan ya zama babban Darakta a hukumar Adana kayan tarihi ta jihar Katsina a shekarar 1994. Sannan yayi shugaban hukumar kula da tsaftace muhalli ta jihar Katsina Katsina a shekarar 2005. Alhaji Muhammadu Gidado ya karbi lambobin girma da shedar yabo da dama.

Sarkin Musawa Muhammadu Gidado mutum ne mai hakuri da son cigaban tallakawa. Ya na kishin ganin kasar Musawa ta cigabaya kan tsaya yaga ya taimaki talakawansa musammana abin da ya shafi kare hakkinsu .ya rasu ya bar ya ya biyu matan aure da kuma kanne.
Ya rasu a ranar Talata 1 ga watan satumba 2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here