BINCIKEN APC KATSINA: ZIYARA TA GIDAN MALAM

0
234

Suleman Chiroma

Bayan sama da wata daya bamu samu amsar wasikar da muka aika wa jam’iyyar APC ba, ta hannun shugaban ta na jiha, muka sake zama mitin aka tsayar a sake rubuta masu takardar tuni. Ni aka ba don in kai ta. Babban edita ya kalle ni yace kai zaka sake zuwa, dama talakkan kasar ku ce, duk aka bushe da dariya.

Da na je ofis din APC karo na biyu, wajen karfe sha biyu rana, na iske wani dattijo bakin hawa saman benen ofis din ya tokare kafar sa hanyar hawa benen.

Nayi masa sallama nace takarda ce, na kawo, ya miko mani hannu in bashi na mika masa na bashi biro da takarda ya sanya mani hannu ya karba.

Na tambaye shi don Allah ina zanga ciyaman? Yace, “gida” nace na gode.

Ina fitowa bakin hanya na samu mai mashin din haya nace masa, gidan ciyaman na APC zaka kaini, “na ina?” Nace gidajen da yawa ne? Yace e”h akwai tsohon gida, akwai gidan amarya akwai babban gida” nace kaini dukkanin su, muna tambaya inga ko na dace yana cikin daya, in samu ganinshi.

Muka fara zuwa tsohon gida aka ce baya nan, nayi ma ginin kallon tsaf muka wuce gidan amarya nan ma akace bayanan na kalle shi a tsanake, muna zuwa babban gidan aka ce yana a ciki na sauka na sallami dan mashin din ya tafi.

Na je wajen masu gadin nace in son magana da shugaban jam’iyya ne, aka ce da farko dai ba a shiga gidan sai ya bada sunanka, sai dai ka zauna nan in ya fito kayi sa a ya kalle ku in baya uzuri ya tsaya ya sauke gilas yayi magana da wanda yake son zantawa da shi.

Na samu waje na zauna tare da wasu da na gani suma sun zauna suna jiran wannan tsammanin.
Ina ta mamaki wane irin shugaban jam’iyya ne wannan? A duk yawo na na aikin jarida, shugabanni jam’iyya suna zama masu saukin kai ga jama’a ne, suna samar da wajen haduwa da Al’umma gidansu bude yake Ofis kuma wangame yake.

A katsina ofis ba kowa gida kuma garkame ga wasu zaratan masu gadi suna ta mazurai ‘yan jiran ace su aikata.

Nan na zauna da sauran ‘yan jira, ina sauraren labarai daga abokan zama ina kuma lura da abin da ke zuwa a shigi da ficin gidan.
Na lura mai katuwar mota kadai ake bude ma wa, ko su wasu sai an buga waya, sai kuma wadanda aka Kira.

Awata uku, naji yunwa ta fara kama ni, na baro kofar gidan, gidane na alfarma na fada a bada labari kuma yadda naga gidajen guda uku, nan na tabbatar da karin maganar nan da ke cewa dare daya Allah kanyi Bature da Allah ya sanya nayi ido da ido da shi da tambaya hudu kacal zan masa, cikin su shi ne tsakanin shi da Allah ya ya gina wadannan tankama tankaman gidajen guda uku cikin shekaru biyar? Da sana’arsa ce ta cinikin motoci ana bashi kamasho? ko ko?

An tabbatar mani duk mataimakan shi na jam’iyya a jiha da zababbun shugabannin jam’iyya na jiha babu mai gidan da ya kai kudin da aka kashe wajen hada wutar lantarki da ruwa na gidajen shi.

Ya mu’amalarsa da jama’ar gari? Wasu na yabawa wasu na kushe, sai dai naji cewa mai martaba Sarkin Katsina, ya zanta a lokacin da aka yi nadin Madugun Katsina Alhaji Muntari Lawal shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina.

Mai martaba Sarkin Katsina, ya kalli shugaban jam’iyyar yace kana nan kuwa shekaru ban ganka ba, nan wasu suka rika bada hakuri.

Wannan shi ne labari na, akan abin da na sani na kokarin jin ta bakin shugabannin jam’iyyar APC akan binciken da muka kammala, saura sakin rahoton ga al’umma su karanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here