Sahel sanity sun kakkabe ‘yanbindiga sama da 100

0

Shuaibu Ibrahim Gusau
Rundunanar operations Sahel sanity sunsami nasarar kakkabe ‘yanbindiga sama da 100 tare da kwato dabbobi sama da dubu biyar a lokacin da suke gudanar da atisayensu a jihohin katsina da zamfara da sokoto.

Hakan ya fitone daga bakin mai magana da yawun rundunar kanal Aminu liyasu a lokacin da yake yiwa manema labaru bayani a Faskari, ya kara da cewa Kawo yanzu, a jimlar atasayen da ya gudana, dakarun sunyi nasarar kakkabe yan bindiga dadi 100, sun kuma kwato shanun sata 3,984, kananan dabbobi 1,627 gami da rakuma 3.

Haka kuma, dakarun sunyi nasarar ceto mutane 107 da akayi garkuwa dasu game da cafke masu baiwa yan bindiga dadi bayanai guda 20, masu safarar miyangun makamai – 6, masu cinikin dabbobin sata – 13 da masu safarar kayan masarufi zuwa wajen yan bindiga dadi – 32.Bugu da kari, an rugurguza maboyar yan bindiga dadi – 81 cikinsu harda zangon fitinannen dan bindiga dadi da ake kira da suna DANGOTE.

See also  Zamu hada karfi da karfe da dukkanin hukumomin tsaro na jihar Katsina - Kwamishina

Bugu da kari, an kame dunbin makamai wanda suka hada da bindiga kirar AK 47 – 43, bindiga mai jigida kirar GPMG -1 da bindigogi kirar gida- 100, gami da harsasai na bindigar AK 47 guda 3,261 da harsasan indigo kirar gida – 151.

Iliyasu ya kara da cewa dakarun sun yi nasarar kawar da farmakin yan bindiga dadi kan jama’a har guda 74 da kuma farmakin masu garkuwa da mutane har guda 54.

Ya ce Haka kuma an bukace su da su kara kaimi wajen cimma Karin nasarorin a nan gaba, haka kuma an bukaci jama’a da suci gaba da baiwa Sojojin hadin kai da bayanai kan ayyukan yan ta’adda domin kawo karshen su baki daya.

Iliyasu ya Kara da cewa Sojan kasa ta Najeriya na tabbatarwa da jama’ar yankin Arewa maso Yamma da matsayinta kan kawar da duk wani yanayi da zai kawo nakasu ga rayuwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here