JARIDUN TASKAR LABARAI;
MATSAYARMU A BINCIKEN APC KATSINA.
Ana amsar mulki ne ta hanyoyi hudu, kisan gilla ga masu mulki, juyin juyahali, juyin mulki, sai kuma zabe ta hanyar dimokardiyya.
Mu a Taskar Labarai, mun yi imani da amincewa, hanya ingattata ta dora shugaba a Nijeriya, shi ne zabe a kyale jama’a su zabi wanda suke so ba tare da wata tsangwama ko tursasawa ba.
Mun amince cewa a wayar da kan mutane su zabi mutane na gari wadanda zasu wakilcesu su yi masu aiki tsakani da Allah.
Babu yadda zaka iya fitar da dan takara na gari sai in akwai jam’iyya da kuma jami’anta na kwarai idan shugabannin jam’iyya bara gurbi ne, to zasu kawo mana bara gurbi su nemi mu zabe su.
A zaben 2019, jaridun Taskar Labarai sun yi adawa da wanda jam’iyyar PDP ta tsaida, mun fallasa shirin da suka sako shi, mun bishi har gidan shi mun masa labari, mun bishi har garin su mahaifarshi mun masa labari, duk motsin shi yana zama labari a wajenmu.
Ana gama zabe mun rika fadin duk wani abin alheri da muka samu labarin yayi, don bamu da komai tsakanin mu da shi.
A zaben 2019, tun a zaben fitar da gwani mun rika kalubalantar takarar wasu yan takarar, misalli sanata Barkiya, mun je har Barkiya mun yi labari har da hotuna, ranar zaben har barkiya muka je gaban mu ya jefa kuri’a.mukayi masa labari har da bidiyo.
A zaben 2019 tun a zaben fitar da gwani mun rika goyon bayan dan takara ne wanda muka natsu da shi a kowace jam’iyya, a babban zabe kuma mun rika goyon bayan dan takarar da muke ganin sh ine alheri ga jama’a.
Jam’iyya ita ce tsanin hawa karagar mulki a dimokaradiyya, ita ce zuciya wadda in ta gyaru jiki ya gyaru in ta baci jiki ya baci, ita ce liman a sallah.dole ne kowa ya fito don gyaran jam iyya.
Muna ciki tsundum wajen ganin jam’iyyar PDP ta samu shugabanni na gari, mun rubuta labarai sosai akan haka ‘yan PDP sun san wannan.
Yanzu kuma mun dauri damarar ganin cewa a APC shugabannin ta adalai ne, zamu yi wannan ko a bayyane ko kuma ta karkashin kasa, ko duka biyun.
Mun fara mu kadai, amma mun fara samun magoya baya, duk wani rubutu da zamu yi zamu tabbatar ya cika ka’idar bincike a aikin jarida, za kuma mu ba kowa hakkinshi na ya fadi nasa bangaren.
Binciken da mukayi wanda zamu fara fitar da rahoton a satin da zamu shiga, insha Allah sai da muka dau tsawon watanni muna yi, da muka kammalla sau biyu muna rubuta wasiku ga shugabannin jam’iyyar don su fadi nasu bahasin.
Amma basu bamu amsa ba, tsakanin wasikar farko zuwa ta biyu wata daya, tsakanin ta biyu zuwa yanzu wata daya, sama da kwanaki sittin don haka, mun basu damar su.
Rahoton da zamu saki yana da bangare uku, kowanne zamu sake shi lokaci daban-daban. Bukatar mu, a gyara jam’iyyar APC yadda zata kawo mana mutanen kirki a zaben 2023.