Kwamishinan Ilimi ya sauke kungiyar shugabannin makarantu sakandare a zamfara

0
208

 

Kwamishinan Ilimi ya sauke kungiyar shugabannin makarantu sakandare a zamfara

Shu’aibu Ibrahim Gusau

Kwamishinan Ilimi na jihar zamfara, Alhaji Ibrahim Abdullahi ya bada umurnin sauke shugabannin makarantun sakandare dake fadin jihar sakamakon samunsu da wuce lokacinsu na ka’ida da doka ta basu.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa wakinmu Karin haske, bisa dalilinda ya aka sauke su a ofishinsa dake gusau.

Ya kara da cewa su wadanda suke kan mulki bisa ka’ida shekara hudu ya kamata suyi su sauka, amma sai da suka kwashe shekaru Tara akan mulki.

Yace bisa Wannan dalili yasa aka saukesu ” muka Nemo wadanda suka dace muka sanyasu, kuma a cewarsa a ranar litinnin dinnan zasu mika mulki, zuwa ranar laraba a a rantsar dasu.

Alhaji Ibrahim ya Warware zare da abawa kan shugabannin da ake cewa ya Kora “ya ce ba koransu mukayiba munyi masu kakkausar gargadine na jan kune don an samesu da laifin barin wurin aiki batare da wani dalili ba “inji shi

Yace bugu da Kari “kwamitin da muka nada Sun tafi makarantar sakandare na jeka ka dawo dake Bukuyum, kasan lokacin jarrabawa ne sai suka samu babu kowa ga dalibai suna jarrabawa amma babu shugaban makaranta babu mataimaki babu wadanda ya kamata ” inji shi

Yace haka abin yake da suka tafi Anka suma abin be canza zani ba ,hakan yasa muka kirasu, “Da nace a dakatar dasu domin a lokacin Raina ya baci, amma da yake muna tattaunawa ne sai aka kai karshe da cewa mu ja masu kunne ne” yace

Ya kara da cewa amma daga yanzu duk Wanda muka samu da laifi Irin Wannan to zamu daukin matakin da yadace, babu bata lokaci, don haka sudai suna nan suna ci gaba da aikinsu babu matsala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here