HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA A YANKIN BATSARI, ANA SAMUN SAUKI?

0

HARE-HAREN ‘YAN BINDIGA A YANKIN BATSARI, ANA SAMUN SAUKI?
Aliyu batsari
@ taskar labarai
Tun bayan mummunan harin da suka kai kauyen Zamfarawa dake gabaccin Batsari wanda mutanen kauyen ukku suka rasa rayukansu sakamakon artabu da sukayi da ‘yan bindigar da suka kai hari kauyensu da nufin satar shanu, kodayake suma sun samu asarar rayukansu, wannan ya faru kimanin makwanni biyar da suka gabata.

Daga nan ba a kara samun kazamin hari ba sai dai jama’a na kokawa da harin sari ka noke da suke kaiwa wasu yankunan dake cikin lunguna kamar su Garin Labo, Dangeza, Sabon gari, Shekewa da sauransu.

To amma yanzu abun yana neman sake kunno kai domin ko a yammacin yau lahadi 6/9/2020 sun budewa wata motar ‘yan kasuwa da suka dawo daga kasuwar Jibiya, lamarin ya faru a kan hanyar Batsari zuwa Jibiya gab da shiga kauyen Gobirawa.Sun yi garkuwa da wani dan kasuwa mai suna Alhaji Ibrahim mai kwanoni da wasu da bamu iya tantancewa ba.

Haka kuma, jiya sun dauke wani mutumin kauyen Biya Kikwana mai suna Alhaji Abdulhamida a gonarshi dake arewa maso yammacin Gobirawa tare da wasu da bamu tabbatar ba.

Haka dai lamarin ke faruwa jefi-jefi, domin ko ranar alhamis sun tare ‘yan kasuwa mazauna kauyen Garin Labo suka kwace masu kudi da wayoyin hannu.

Ga kuma satar babura da ya zama ruwan dare da zaran ka fita yammacin Batsari da babur dinka ba lalle bane ka dawo da shi domin idan ma ka dawo hannu biyu sai a cigaba da yi maka murna.

Sannan suna bin mutane gonakai suna kwace masu shanun noma idan sunje aikin gona, kuma sun kai hari kauyukan Kurmiyal, Maidoriya da Tashar na Gulle, inda suka fasa shaguna a Kurmiyal kuma suka sace shanu hudu tare da yima wani dattijo dukan kawo wuka, sai dai daga bisani shanun sun kutto.

Maidoriya da Tashar Nagulle kuwa babur daya-daya suka sata. Wannan lamari ya faru cikin satin da ya gabata.
An samu Ragowar Hari na kisan kiyoshi da tada gari a yanki. An kuma samu ragi na garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda.
Wannan ya samu sakamakon addu a ba dare ba Rana da jama a suke gabatarwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here