Rikicin APC a Zamfara: Masu biyayya ga Marafa sun nesanta kansu da shigar da kara kotu

0

Shuaibu Ibrahim Gusau

‘ya’yan jam’iyyar APC( All Progressives Congress) a jihar Zamfara masu biyayya ga Sanata Kabiru Garba Marafa sun nesanta kansu daga karar da aka ce suna kalubalantar jam’iyyar a jihar.

A lokacin da suke zantawa da manema labarai a sakatariyar APC ta jihar da ke Gusau a ranar Talata, wakilan shugabannin APC na unguwanni masu biyayya ga Marafa sun ce an sanya sunayensu a cikin karar da aka shigar ba tare da saninsu ba don haka suka yi tir da matakin da suka bayyana shi a matsayin yaudara.

Daya daga cikin wadanda akayi amfani da sunayen nasu, Malam Shafi’i Musa, Shugaban mazabar Yargaladima a karamar hukumar Anka, ya ce ba shi da masaniyar karar sai kawai aka gaya masa cewa sunansa ya shiga cikin jerin sunayen shugabannin jam’iyyar APC 147 da ke kalubalantar jam’iyyar a jihar.

“A yanzu haka shugabannin mazabu 74 da shugabannin kananan hukumomi 9 kuma har yanzu ana kirga suna shirin kai karar Sanata Kabiru Garba Marafa da Alhaji Surajo Maikatako shugaban jam’iyar bangaran marafa saboda amfani da sunayenmu ba tare da yardarmu ba, ya mu membobin APC ne kuma ba za mu taba shiga wani hali na ruguza zaman lafiyar jam’iyyar ba”in ji shi.

See also  ‘Yan jam’iyyar APC na Kano suna son a hukunta Bashir Ahmad saboda barin jam’iyyar ya tafi kallon buga a gasar cin kofin duniya a Qatar

Ya bayyana kokarin da kwamitin rikon na kasa ke yi a matsayin kyakkyawan mataki na kawo karshen duk wani rikici a cikin jam’iyyar.

Tun da farko, shugaban kwamitin ladabtarwa na mutum 7 da hedkwatar jam’iyyar ta kasa ta kafa, Alhaji Abdullahi Ja’o ya ce kwamitin zai yi aiki ba tare da son rai ba don tabbatar da hadin kan jam’iyyar.

“Za a tuna cewa lokacin da shugabanmu Shugaba Buhari ya kafa kwamitin riko na kasa, ya umarci dukkan mambobin jam’iyyar da ke da rigimar kotu da su janye a matsayin alamar sulhu amma wasu a jihar Zamfara sun ki yin hakan,” in ji shi.

Ja’o ya bayar da tabbacin cewa duk da kin wasu ‘yan jihar da suka yi na dakatar da shari’ar, kwamitin zai bai wa dukkan mambobinsu damar sauraren adalci don tabbatar da cewa jam’iyyar ta zama abin tsoro a jihar,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here