SAKAMAKON BINCIKEN APC: NAWA JAM’IYYA TA TARA A ZABEN 2019?

0

SAKAMAKON BINCIKEN APC: NAWA JAM’IYYA TA TARA A ZABEN 2019?

Muazu Hassan
@Jaridar Taskar Labarai

Binciken da jaridar nan ta dauki tsawon wata uku tana yi, kuma ta dau kwanaki tana jiran amsa daga ofishin jam’iyya na jiha, yana da bangarori daban-daban da rassa da kuma shiyya-shiyya.

Wannan Wanda ya shafi kudaden da jam’iyya ta tara a sayar da fom na zaben fitar da dan takara da kuma sauran zabukan cike gurbi ne .
Kafin wannan rahoton namu babu wanda yasan nawa jam’iyyar ta tara hatta a cikin wasu jami’an jam’iyyun na kananan hukumomi da wasu a jiha.

Mun samu tabbacin abin da muka gano ta bayanai da muka samu ta barauniyar hanya daga hedkwatar jam’iyyar ta jiha da kuma wasu bayanan da muka samu a bayyane ta hedkwatar jam’iyyar ta kasa.

Da bin jerin sunayen ‘yan neman takara da suka sayi fom muna kiran su don tabbatar wa. Ga jadawalin kudaden a jumlace da kuma tsare kamar yadda muka gano.

Kudi uku ake biya idan kana son takara a jam’iyyar APC na farko kudin nagani ina so, na biyu kudin fom na uku kudin jam’iyya, dukkanin kudaden halastattu ne a doka ta kasa da tsarin mulki, don suna cikin hanyar da ake bi don jam’iyya ta samu kudin shiga duk duniya tsarin dimokaradiyya ya amince da shi.

A zaben 2019 a jihar Katsina jam’iyya ta samu kudi kamar haka zaben majalisar dokokin jiha, zaben majalisar tarayya, zaben sanatoci, zaben gwamna da zaben shugaban kasa.

A zaben majalisar dokokin jiha mutane dari da Saba’in da shidda suka sayi fom a duk fadin jihar Katsina. A zaben ‘yan majalisar tarayya mutane sittin da bakwai suka sayi fom a duk jihar Katsina.

A zaben sanatoci mutane goma sha daya suka sayi fom, a zaben gwamna mutum daya ya sayi fom, a zaben shugaban kasa mutum daya daga jihar Katsina.

A kudin na gani ina so, jihar ta tara ma APC kudi har naira miliyan hamsin da takwas, da dubu dari biyu da goma ga dukkanin ‘yan neman shiga takara a matakai guda biyar.

A Kudin sayen fom, jihar Katsina ta tara wa jam’iyyar APC kudi har naira miliyan dari biyar daga dukkanin yan neman shiga takara guda biyar daga jihar Katsina.

A kudin jam’iyya na jiha ‘yan neman shiga takara sun samar wa jam’iyyar ta jiha kudin shiga har naira miliyan arba’in da biyu da dubu dari hudu. Daga dukkanin matsayi biyar da ake neman a yi takara a cikin su.

A jumlace ofishin jam’iyya na jiha ya samar wa da jam’iyyar APC kudin shiga a takarar 2019 a matsayi biyar da ake nema kudi har naira miliyan dari shidda da dubu dari shidda da goma.( 600,610,000)

A zaben cike gurbi an yi zaben cike gurbi a mazabun dan majalisar tarayya guda biyu, an yi na Sanata guda daya, an yi na Dan majalisar jiha guda biyu, sune mashi da Dutsi. Sai Sanatan Daura, sai ‘yan majalisun jiha na Bakori da Sabuwa.

A wadanna zabubbukan guda hudu, jam’iyyar APC ta Katsina, ta samar da kudin shiga har naira miliyan sittin da shidda da dubu dari uku da tamanin.

Kudaden da jam’iyya ta caji kowane mai neman takara.
Dan majalisar jaha.

Kudin fom N750,000
Na gani iina so N100,000
Kudin jam’iyya N200,000

Yawan wadanda sukayi sayi fom na shiga takarar 2019 a majalisar jiha, su dari da Saba’in da shidda.

Majalisar Tarayya
Kudin fom N3,500,
Na gani ina so , 330,000
Kudin jam’iyya, 200,000
Yawan wadanda suka Nemi shiga takara 67.

Sanatoci
Kudin fom N6,000,000
Nagani Ina so N1,000,000
Ofishin APC N200,000
Mutanen da suka tsaya takara 11

Gwamna
Kudin fom N22,500,000
Na gani ina so N2,500,000
Kudin jam iyya N200,000
Mutum daya ya saya

Shugaban kasa
Kudin fom N45,000,000
Nagani ina so N5,000,000
Kudin jam iyya , 200,000.
Mutum daya ya saya daga katsina.
Kowace takara zakayi,daga unguwar ku kake farawa har zuwa tarayya.don haka kudin fom din shugaban kasa ana daukar shi daga katsina yake in ya fito takara.

A zaben cike gurbi

Yan takara uku suka sayi fom a zaben Mashi da Dutsi na dan majalisar tarayya.

A zaben sanata yan takara hudu suka sayi fom na shiyyar Daura a zaben Dan majalisar tarayya, Kusada/Kankia/Ingawa ‘yan takara uku suka sayi fom.

A zaben Dan majalisar jiha na Bakori ‘yan takara shidda suka sayi fom, a zaben Dan majalisar jiha Sabuwa ‘yan takara bakwai suka sayi fom.

Tsakanin zaben 2019 da na cike gurbi jam’iyyar APC ta Katsina ta samar wa da APC kudin shiga har naira miliyan dari shidda da sittin da shidda da dubu dari tara da chasa in.( 666,990.000)

A tsarin mulkin jam’iyyar kowane bangare yana da kason da zai samu, jiha, karamar hukuma, yankin da kuma babban ofishin jam’iyyar na kasa.

Wannan shi ne bayanin da muka so shugabannin jam’iyya na jiha suyi mana,nawa suka samu ya suka yi dasu? Amma bamu samu wannan bayanin ba duk da wasikun da muka aika, har guda biyu da sakon wayar hannu da muka aika, duk ba amsa.

Amma dai a bayyane take ofishin jam’iyya na jiha. ko fenti ba a sake masa ba, kujerun sun karairaye, kyawaren a jingine wajen kamar anyi yaki ba aci nasara ba.

Wannan shi ne rahoton binciken kudin sayen fom da aka tara a zaben 2019 da na cike gurbi daga jihar Katsina ga jam’iyyar APC.

Rahoton ya kammala da taimakon Suleman Chiroma, Umar Abubakar, Abdurrahaman. A . Muazu Hassan, da Badiyya Hussaini.
_______________________________________________
Taskar labarai, jarida ce dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma ‘yar uwarta Turanci The Links News dake a www.thelinksnews.com. duk sako ga 07043777779. kira ko whatsap email katsinaoffice@yahoo.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here