Rundanar Operation sahel Sanity sun sami Karin wa’adi zuwa watan sha Biyu 2020

0

Daga shu’aibu Ibrahim Gusau

Sojojin Najeriya da suke karkashin Rundunanar Operation Sahel Sanity, sun sami Karin wa’adi zuwa watan sha Biyu na wannan shekara ta 2020.wanda ke yaki da ‘yan ta’adda da satar mutane da satar shanu a yankin Arewa maso Yamma, zuwa watan Disamba.

Babban hafsan sojojin, Laftana-Janar. Tukur Buratai, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a sansanin sojoji Nageriya na 4, dake Faskari,a karamar hukumar faskari ta jihar Katsina.

Buratai ya ce bayan nazari sosai game da aikin, wanda ake yaki da ‘yan ta’adda da masu satar mutane da satar shanu a yankin Arewa maso Yamma.

Ya ce an ga ya kamata a fadada shi don ci gaba da nasarorin da aka samu a cikin wannan lokacin da kuma ba sojoji damar kawar da duk wani nau’i na ta’addanci daga yankin,ya ce an kuma fadada aikin zuwa yankin Arewa ta Tsakiya don tabbatar da zaman lafiya a duk sassan kasar.

Shugaban sojojin yace za mu ci gaba da inganta har kar tattara bayanai, ya ce “Kodayake sojojin da ke cikin yakin sun sha wahala saboda yanayin kasa , duk da haka sun sami damar shiga wasu yankuna a yayin arangamar, amma sojojin Najeriya sukadai suka san halin da suke ciki,” in ji shi.

Ya kuma yabawa jihohin da ke karbar bakuncin mayakan Kamar Zamfara da Katsina da sokoto don ci gaba da samun goyon baya da hadin kai musamman a bangaren musayar bayanai.

Ya kuma bukaci al’ummomi su kasance a shirye don fallasa masu aikata laifi a tsakanin abokansu da danginsu, yace idan ba haka ba, sakamakon zai dawo gare su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here