Gwamnatin Tarayya za ta fito da Shirin Yaƙi da Yunwa

0

Gwamnatin Tarayya ta na nan ta na ƙoƙarin fito da shirin Yaƙi Da Yunwa, wato Zero Hunger Round Table, don rage wa al’ummar Nijeriya raɗaɗin fatara da yunwa.

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a wajen taron Cibiyar Samar Da Abinci ta Ƙasa (National Food Security Council) wanda aka yi a ranar Alhamis, 10 ga Satumba, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A jawabin da ta gabatar a taron, Hajiya Sadiya ta bayyana cewa za a fito da shirin ne a matsayin wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi na rage yunwa a Nijeriya, wadda zaman dole na annobar korona ya ƙara kambamawa, da nufin kawar da yunwa tare da samar da abinci, inganta samar da abinci mai gina jiki da kuma haɓaka aikin gona ya zuwa shekara ta 2030 tare da haɗin gwiwar waɗanda abin ya shafa.

Ta ce: “Wannan Ma’aikatar ta samar da hanyoyin rage wa jama’a raɗaɗin matsalolin rayuwa ta hanyar samar da abinci cikin gaggawa da kuma hanya mai ɗorewa ta hanyar shirin Magance Yunwa.

“A matsayin ɗaya daga cikin ayyukan wannan Ma’aikata na tabbatar da rage raɗaɗin aukuwar bala’o’i tare da shirin ko-ta-kwana da kuma kai agaji, shirin Inganta Rayuwar Al’umma na Ƙasa (NSIPs) ya taimaka wa aikin Ma’aikatar a matsayin wata hanya ta samar da hanyoyin taimakon jama’a, ciki har da bada abinci ga mutane marasa galihu a dukkan faɗin ƙasar nan.”

Hajiya Sadiya Umar Farouq ta tuno da cewa shirin nan na ciyar da ‘yan makaranta da ke zaman gida da na kai abinci gida (Take Home Rations, THRs) an yi su ne domin samar da abinci ga gidaje mabuƙata guda 127,589 masu yara ‘yan aji 1 zuwa 3 na firamare a makarantun gwamnati a Yankin Babban Birnin Tarayya (FCT) da jihohin Legas da Ogun, yayin da aka kai manyan motoci 164 shaƙe da kayan abinci a jihohi 36 da yankin Abuja a matsayin agaji da aka samu daga Hukumar Kwastam ta Nijeriya.

Ta ƙara da cewa, “Ya zuwa yau dai, sama da tan 41,000 na hatsi daga Rumbunan Ajiyar Hatsi da ake sa ran za su kai ga gidaje sama da miliyan 5 aka miƙa wa gwamnatocin jihohi 19 da Babban Birnin Tarayya. Ana rabon ne ta hanyar hukumar NEMA a bisa umarnin Shugaban Ƙasa.”

Ministar ta ƙara da cewa Shirin Yaƙi Da Yunwa za a yi shi ne tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona da Haɓaka Karkara ta Tarayya da kuma wasu shugabannin kamfanoni masu zaman kan su irin su Tony Elumelu, Tonye Cole da kuma Sahel Consulting, IFPRI, IITA, NESG, FAO, IMMAP, ECOWAS da sauran su.

Ta bayyana cewa hanyoyin da za a bi a aiwatar da wannan Shirin Yaƙi Da Yunwa ɗin sun haɗa da yin amfani da bayanan da aka tattara game da gidajen da ke buƙatar taimako, da haɗin gwiwa, samar da aikin yi da kuma taimaka wa sashen aikin gona tare da inganta hanyoyin da abinci ke bi daga manoma ya kai ga masu sayar da shi, da inganta samar da abinci mai gina jiki, ƙarfafa rumbunan tara abinci tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Aikin Gona da sauran masu ruwa da tsaki a lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here