Jam’iyar APC a zamfara ta bukaci kafa kwamitin bincike na gaggawa da shugaban ‘yansanda ta kasa

0

Daga shuaibu Ibrahim Gusau

Jam’iyyar APC reshen jihar zamfara (All Progressive Congress) karkashin jagorancin shugaban jam’iyar, Alhaji Lawal Muhammad Liman ya yi kira ga Sufeto Janar na ’Yan sanda, Mohammed Adamu da cewa cikin gaggawa ya kafa kwamitin bincike na musamman kan abin da ya bayyana da cin mutunci da bata suna da cinzarafi tare da tsoratar da mambobin jam’iyyar da‘ yan sanda suka yi babu gaira babu dalili a karkashin jagorancin Kwamishinan ’Yan sanda jihar Usman Nagoggo.

Shugaban jam’iyyar ya yi wannan kiran ne a wani taron da ya kira na manema labarai a ofishinsa ,a lokacin da yake mayar da martani game da alkawarin da aka yi musu ta hana su hakkinsu na ‘yancin ‘yan sanda.

Liman ya ci gaba da cewa, kiran ya zama dole sakamakon ganin yadda, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Usman Nagogo ya hada baki da gwamnatin jihar karkashin jagorancin Goveronor Bello Mohammed Matawalle ya kame mambobin APC 17 kuma aka tsare su ba bisa ka’ida ba fiye da awanni 10 tare kuma da sakinsu ba tare da anbi wani sharadi ba.

Liman ya ci gaba da cewa, jam’iyyar ta sanar da dukkanin masu ruwa da tsaki kan lamarin a matakan kasa kan matakan gaggawa da za a dauka don tabbatar da lafiyar dukkan mambobin jam’iyyar a jihar.

A cewarsa, mambobin jam’iyyar za su ci gaba da kasancewa ‘yan kasa masu bin doka tare da gargadin mambobinsu da su guji duk wani nau’i na karya doka da oda da ka iya haifar da rikici a jihar , ya ce shugabancin jam’iyyar zai ci gaba da jajircewa don yaki da‘ yancinsu na halal.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here