Kungiyoyin Farar Hula 180 a Kano sun bukaci a janye karin Farashi da aka yi

0

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gamayyar kungiyoyi fararen hula 180 a Kano sunyi Allah wadai da karin farashin man fetur da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta yi daga 148 zuwa naira 151 akan kowace lita.

Shugaban hadaddiyar kungiyar kwamared Ibrahim A. Wayya ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano,

Kwamred wayya ya ce abin takaici ne kwarai idan akai laakari da yadda talaka ke cikin kunci amma gwamnati ta kara kudin Man fetur da karin wutar lantarki 100 bi sa 100

Haka kuma Kwamared wayya ya nuna takaicinsa akan yadda babban bakin kasa CBN ya kara yawan cajin da ya ke wa masu ajiyar kudi a Bankuna wanda haka zai shafi Talaka da masu karamun karfi,

Ya yi kira da babbar murya akan gwamnati ta dawo da asalin farashin mai da na lantarki, matukar baa dawo da farashin ba za su dauki matakin da ya dace a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here