Zaɓen Edo: lZa a hukunta masu laifi,
inji shugaban INEC
Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa, wato INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani wanda aka kama da aikata laifi a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar 19 ga Satumba, 2020.
Farfesa Yakubu ya yi gargaɗin ne a lokacin babban taron da ya yi da dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen wanda aka yi a Benin, babban birnin jihar, a ranar Litinin.
Ya lissafa wasu daga cikin laifuffukan kamar haka: sayen ƙuri’a, ƙwace akwatin zaɓe da cika shi da ƙuri’u, kaɗa ƙuri’a sama da sau ɗaya, fizge kayan zaɓe tare da kautar da su ta wata hanya, da sauran su.
Ya ce: “Tilas ne a ƙyale mutanen Edo su zaɓi duk ɗan takarar da ya kwanta masu a rai ba tare da an ba su kuɗi ko an yi masu wata barazana ba.
“Hukumomin tsaro sun tabbatar mana da cewa ba za a ƙyale ‘yan daba da masu ɗaukar nauyin su su samu sukunin watayawa don kawo ruɗani a zaɓen ko cibiyoyin tattara sakamakon zaɓen ba.’’
Farfesa Yakubu ya kuma bayyana cewa babbar hedikwatar INEC za ta sa ido a kan yadda zaɓen ke gudana a duk faɗin jihar ta hanyar manhajar Zoom da aka girke a wani babban zaure a Abuja.
“Wannan zaure mai Zoom zai ba mu damar mu rinƙa samun rahotanni kai-tsaye daga wuraren da ake gudanar da harkokin zaɓen.
Su ma jami’ai da ‘yan sa ido da ‘yan jarida da aka yi wa rajista za a rinƙa kiran su zuwa wannan zauren a kai a kai.
“Ta wannan hanyar, hukumar za ta rinƙa samun sahihan bayanai daga ganau ba jiyau ba a lokacin da zaɓen ke gudana.”
Shugan na INEC ya kuma bai wa jama’ar Edo tabbacin cewa ƙuri’un su za su yi tasiri, ya na mai ƙarawa da cewa ainihin wanda mutanen Edo su ka zaɓa shi ne za a gani a sakamakon zaɓen.
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa hukumar ba za ta yi wani abu domin taimakon ko ƙin taimakon wata jam’iyya ko wani ɗan takara ba.
A cewar sa, “Mun tattara dukkan hankalin mu ne kan yadda mu ke gudanar da aikin mu da kuma ƙa’idojin mu, ba ragi ba daɗi, kuma mun tabbatar maku da cewa zaɓen da za a yi a ranar Asabar zai kasance sahihi matuƙa.”
Har ila yau, Farfesa Yakubu ya bayyana cewa hukumar za ta kai gilasan ƙara girman rubutu da kuma keken rubutu irin na makafi da za su taimaka wa naƙasassu don su ma su yi zaɓen da kan su ba tare da wani ya zo ya na taimaka masu ba.
Ya ce: “An maida tsarin yadda ake zaɓe na INEC bayan faruwar cutar korona zuwa tsarin abin karatun makafi don a tabbatar da cewa kowa da kowa ya shiga zaɓen an yi da shi duk da irin naƙasar da ya ke da ita.”
Shugaban ya kuma bayyana cewa an fasa yin amfani da wani ɓangare na wata komfuta da ake kira ‘z-pad’ a wajen zaɓen.
Ya ce an riga an gama ɗaukar duk wasu ma’aikatan wucin-gadi, kuma ba za yi wasa da ingancin tsarin gudanar da zaɓen ba.
Shi ma a nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Matasa ‘Yan Bautar Ƙasa (NYSC), Birgediya-Janar Shu’aib Ibrahim, ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaɓen da su tabbatar da tsaro da lafiyar dukkan ‘yan hidimar ƙasa da aka tura don yin aikin zaɓen.
Ibrahim, wanda Jami’in NYSC na yankin kudu-maso-kudu, Mista Benjamin Ayodele, ya wakilta, ya gode wa hukumar zaɓen saboda yardar da ta yi da ‘yan bautar ƙasar.
A cewar sa, “Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su kare ‘yan hidimar mu daga kowane haɗari a lokacin zaɓen.”
Shi kuwa wakilin Sarkin Benin, Cif Osato Bazuaye, kira ya yi ga INEC da Sufeto-Janar na ‘Yansanda da su tabbatar da cewa an yi zaɓen cikin adalci, kwanciyar hankali da lumana.
Ya ce, “Mu na so ku ɗabbaka abin tarihi. Ku tabbatar da cewa wannan zaɓe ya na daga cikin waɗanda su ka fi kowanne inganci. Zakaran gwajin dafi ne ga INEC da ‘yansanda da mu kan mu baki ɗayan mu.”