A shirye muke mu bude Makarantu a jihar Kano

0

Sanusi Ƙiru

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Sa’id ya ce a shirye gwamnatin Kano ta ke ta bude dukkanin Makarantun jihar Kano, kwamishinar ya bayyana hakan ne yayin bude wani taron bita da aka shirya wa shugabannin makarantun firamare da sakandare a jihar kan matakan kariya daga cutar COVID-19 a Kano ranar Talata.

“Wannan taron ya zama wajibi kasancewar mun fara shirin bude makarantu kamar yadda Kwamitin Kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa kan yaki da cutar ya umarta.

“kuma Tuni muka yi wa makarantu 538 feshin magani, ciki har da masu zaman kansu; babu wata jiha da ta yi makamancin wannan hobbasan a duk Najeriya”, inji Kwamishinan.

See also  EFCC ta kama wasu mutane 28 da ake zargi da damfarar yanar gizo a Nasarawa

Sannan ya kara da cewa ma’aikatarsa ta samar da dukkannin kayayyakin kariya da ake bukata a makarantun lokacin da aka fara bude su a shirye-shiryen rubuta jarabawar WAEC ga dalibai masu kammala sakandare.

Kazalika, kwamishinan ya kuma ce gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan hudu wajen ciyar da dalibai ‘yan makaranta a jihar da ma sauran bukatu.

Daga nan sai ya ja kunnen shugabannin makarantun kan su tabbatar suna ba daliban abinci mai inganci, inda ya ce zai rika kai ziyarar ba-zata don tabbatar da hakan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here