Kotu ta bada umarnin a kaiwa Malam Aminu Daurawa Sammaci

0

Malam Aminu Daurawa

Daga Ibrahum Hamisu, Kano

Alkalin kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Shahuci a jihar Kano, Malam Garba Kamilu ya ba da umurnin a lika wa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sammaci a kofar dakinsa, ko kuma duk wani waje da dole zai gani sakamakon yaki yarda a hadu da shi a mika masa takardar sammaci.

Sheikh Dauda Lokon Makera ne dai ya yi karar Sheikh Daurawa bisa wasu tuhume-tuhume da yake masa a kan shirin Tambaya Mabudin Ilimi.

Shirin Tambaya mabudin Ilimi dai ne shiri ne da ya yi fice a gidajen Radiyon kasar nan da shekh Dauda yake ikirarin shi ne ya kirkiro shirin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here