Mun gama dukkan shirye-shiryen zaɓen Edo

0

Mun gama dukkan shirye-shiryen zaɓen Edo, inji INEC

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta kammala duk wani shiri da tsari da ake buƙata don tabbatar da an yi zaɓen gwamnan Jihar Edo cikin nasara a ranar Asabar ɗin nan.

Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Alhamis a Abuja.

Okoye ya ce INEC ta gama shirya wa zaɓen tsaf.

Ya ce duk wasu kayan aiki marasa haɗari da aka tanadar don zaɓen na Edo an gama kai su cibiyoyin zaɓe tun cikin Agusta.

“Kayan aiki masu hatsari, wato irin su fom-fom na rubuta sakamakon zaɓe da kuma takardun ƙuri’u, waɗannan sun isa Jihar Edo ne a ranar Litinin,” inji shi.

“Jiya (Laraba), an yi taro da dukkan jam’iyyun siyasa kan yadda za a duba yadda ake gudanar da zaɓen.

“Su kayan aikin sun bar harabar Babban Bankin Nijeriya ne a yau ɗin nan (17 ga Satumba) zuwa dukkan ƙananan hukumomi, kuma waɗannan kayan an rarraba su ne bisa tsarin wuraren da aka yi rajista.

“Mu na da wuraren da aka yi rajista guda 192 a Jihar Edo ko kuma abin da za ka kira unguwanni. Saboda haka, an rarraba waɗannan kayan aiki a bisa tsarin unguwannin, sannan kuma dukkan ƙuri’un da fom-fom da za a rubuta sakamako an yi masu kalolin da kowacce ta dace da ƙaramar hukumar ta.”

Okoye ya ƙara da cewa hukumar ta kuma yi wani tsari na sufuri don magance matsalar samun tsaiko wajen kai kayan aiki zuwa cibiyoyin zaɓe a ranar zaɓe.
Ya bayyana cewa tunda INEC ba ta da wadatattun motoci da za su yi aiki a ranar zaɓen, ta kan ɗauko hayar motoci ne daga ƙungiyar ‘yan yuniyan (NURTW) da ƙungiyar mamallaka motocin haya, wato NARTO, kuma kowacce an ɗau bayanin ta.

Sai dai Okoye ya lura da cewa wasu daga cikin su ba a ganin su a ranar zaɓen duk da yake an biya su rabin kuɗin jingar da aka yi da su.

Ya ce, “Abin da mu ka yi shi ne mun tura motocin mu ƙirar Hilux daga jihohi maƙwabta waɗanda su ba su da zaɓe a ranar, saboda mu yi amfani da su idan an samu matsala irin wannan.

“Na biyu, akwai wasu ƙananan hukumomi ƙalilan waɗanda ke cikin yankin ruwa a Jihar Edo. Don haka mun tuntuɓi rundunar ‘yan sandan ruwa da ta sojan ruwa, waɗanda za su samar da jiragen yaƙin ruwa don kare wasu ma’aikatan mu da za su yi aiki a waɗannan yankunan.

“Mu na aiki tuƙuru don tabbatar da cewa ba mu da irin wannan matsalar wajen raba kayan aiki a ranar zaɓen.’’

Okoye ya ƙara da cewa hukumar ta kammala horas da dukkan ma’aikatan ta na zaɓe, yayin da horaswa domin tattara sakamako daga unguwanni da ƙananan hukumomi da na jiha, wanda a kan bar shi har sai ya rage biyu kafin ranar zaɓe, shi ake gudanarwa a yanzu.

Bugu da ƙari, ya ce babu malamin zaɓe ko ɗaya da aka ɗauka daga kowace babbar makaranta da ke cikin Jihar Edo, sai dai waɗanda ke wajen jihar.

Ya ce, “Saboda haka a game da wannan zaɓen, hukumar ta gama shirya komai. Mun kammala dukkan tsare-tsare da abubuwan da za a yi don gudanar da wannan zaɓen.

“Kamar yadda ku ka sani, mun tura Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe (Resident Electoral Commissioners, RECs) guda biyar don su bada gudunmawa ga shi kwamishinan zaɓe da ke Edo. Kuma mun tura manyan kwamishinoni na ƙasa (National Commissioners) guda uku domin su ma su je su bada tasu gudunmawar. Saboda haka mun shirya tsaf.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here