Buhari ya yi gargaɗi kan siyasar ‘a-mutu-ko-ai-rai’
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da jami’an tsaro da su yi aiki tsakanin su da Allah a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Edo a ranar Asabar ɗin nan.
A cikin saƙon da ya aike wa da masu zaɓe da jam’iyyun siyasa da jami’an zaɓe da na tsaro, shugaban ya kuma yi gargaɗi kan abin da ya kira “tunanin siyasa irin na ko-a-mutu-ko-ai-rai.”
Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan al’amurran aikin jarida da yaɗa labarai, Malam Garba Shehu, shi ne ya bada takardar shawarar da shugaban ya bayar a Abuja inda ya ruwaito Buhari ya na faɗin: “Na yi matuƙar sadaukar da kai na ga tabbatar da zaɓe cikin adalci, to amma tawa sadaukarwar ba ta wadatar ba ita kaɗai idan sauran masu ruwa da tsaki da ke wajen zaɓen ba su bi ƙa’idoji ba.
”Ina so in ga an ɗaga darajar dimokiraɗiyya a ƙasar nan a kowane mataki, amma hakan ba zai samu ba idan su ‘yan siyasa sun hau matsayin a-mutu-ko-ai-rai don kawai su samu mulki ko ta halin ƙaƙa.
“Tunani irin na a-mutu-ko-ai-rai a siyasa barazana ne ga zaɓe cikin adalci da kwanciyar hankali domin su ‘yan siyasar sun fi maida hankali ne ga cin zaɓen maimakon su damu da samuwar sakamako cikin adalci wanda zai nuna buƙatar mutane masu zaɓe.”
Shugaban ya yi kira ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takarar su da su bi doka da oda.
Ya shawarci jami’an zaɓe da na tsaro da “su kasance ‘yan baruwan mu don tabbatar da an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali kuma cikin adalci. kuma su guji aikata duk wani abu da zai iya ɓata darajar zaɓen.”
Ya ce: ”Gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali da adalci ya na daga cikin manyan abubuwan da na tsare a dimokiraɗiyyar mu, kuma ina so wannan sadaukarwar ta kasance ɗaya daga cikin gadon da zan bar wa ‘yan baya idan na bar mulki.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Edo a gobe Asabar.
Haka kuma ya ruwaito cewa ɗan takarar jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu, da na jam’iyyar PDP Godwin Obaseki, waɗanda su ne manyan ‘yan takarar da za su gwabza, sun riga sun rattaba hannu a kan wata takardar yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a zaɓen.