Shugaban Jami’ar Gusau
Daga Shuaibu Ibrahim Gusau
Kungiyar (JAC) ta Jami’ar Tarayya da ke Gusau sun nesanta kansu daga wata takardar koke da aka rubuta a kan Mataimakin Shugaban Jami’ar,
Hakan ya fitone cikin wata takarda wadda ke dauke da sa hannun jami’in hurda da jama’a, na jami’ar mal Umar Usman, ya kara da cewa “Mu da membobinmu ba mu da wata alaƙa da wannan koke kuma mun gamsu sosai da yadda shugaban jami’ar ke Gudanar da Jami’ar.
Ya kara da cewa wadannan koke-koken ba mambobimmu ne na Kungiyoyin Kwadago a Jami’ar ba”, in ji Kungiyoyin
Ya kara da cewa membobin Kungiyar na jami’a wanda shine rukuni na uku a Jami’ar ban da Majalisar da Dattawa da kuma mafi girma a bangaren membobin ma’aikata, yace sun kada kuri’ar amincewa ga mambobin Majalisar Dattawa ta zaba don wakiltar su a ciki har da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Magaji Garba.
Shugabannin Kungiyoyin Kwadago sun fitar da wata sanarwa na bayan taron gaggawa da suka yi a ranar Alhamis 17 ga Satumba, 2020 sun sanya hannu kan matsayar kungiyoyin kwadago kan batun takardar koke da aka ce mambobin jami’ar da abin ya shafa suka rubuta.
Kungiyoyin kwadagon, duk da haka, sun nuna rashin jin dadin su game da yadda wasu mutane ke da niyyar kawo cikas ga dorewar zaman lafiya jami’ar.