Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Godwin Obaseki, shi ne ya lashe zaɓen gwamna da aka yi a Jihar Edo jiya Asabar, 19 ga Satumba, 2020, inji Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
INEC ta bayyana haka ne a cibitar tattara sakamakon zaɓen da ke Benin, babban birnin jihar, a yau.
Obaseki ya doke abokin karawar sa na kurkusa, wato Pastor Ize-Iyamu na jam’iyyar APC.
Alƙaluman sakamakon zaɓen da INEC ta bayar sun nuna cewa Obaseki ya samu ƙuri’u 307,955 yayin da Ize-Iyamu ya samu ƙuri’u 223,619.
Wannan sakamakon ya nuna cewa ɗan takarar na APC wanda ya samu ɗaurin hindin tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya sha kayen bazata tare da rinjaye mai yawan haske.
Ejan ɗin APC a wajen cibiyar tattara sakamakon zaɓen da ke Birnin Benin ya ƙi amincewa ya rattaba hannu a kan takardar sakamakon. Ya ce ba a ba shi izinin ya sa hannun ba, wanda hakan na nuna cewa kila su je kotu nan gaba.
Masu sa ido a zaɓen sun yaba wa INEC kan yadda ta gudanar da zaɓe mai inganci. Shi kan sa Gwamba Nyesom Wike na Jihar Ribas a jiya ya ce hukumar zaɓen da jami’an tsaro sun yi rawar gani. Kuma Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan yadda bai nuna bambanci a zaɓen ba.
Shi ma Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, a jiyan ya yabi yadda aka gudanar da zaɓen. Ya ce ‘yan Nijeriya sun ba maraɗa masu cewa za a yi hargitsi kunya.
Rahotanni sun ce daga sakamakon da aka bayar, akwai bambanci tsakanin yawan ƙuri’un da aka kaɗa da yawan sunayen masu zaɓe da aka yi wa rajista a wasu ƙananan hukumomin. Hakan ya nuba cewa wasu masu zaɓen ba su gita wajen yin zaɓen ba saboda gudun kada a yi tarzoma.
Sai ga shi an yi shi salin alin, an gama lafiyacin ban da wasu wurare ƙalilan da aka tada jijihar wuya wanda nan da nan jami’an tsaro su ka shawo kan lamarin.
A wata sabuwa, Ƙungiyar Jam’iyyun Siyasa ‘Yan Haɗin Kai, wato Coalition of United Political Parties (CUPP), ta yaba wa INEC kan rashin nuna ɓangaranci da ta yi a zaɓen na Edo.
Kakakin ƙungiyar, Mista Ikenga Ugochinyere, ya faɗa cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja cewa matsayin hukumar wata alama ce da ke nuna dattaku a tsarin gudanar da zaɓe a ƙasar nan.
Ugochinyere ya kuma yaba wa ma’aikatan INEC waɗanda ya ce sun ƙi yarda da buƙatar wasu ta a murɗe sakamakon zaɓen, ya ce hakan da su ka yi abin yabo ne.
Ya bayyana nasarar Obaseki da sunan nasarar da ikon jama’a ya nuna.
Ya ce: “Ba shakka wannan nasara ce da aka sha wuya kafin a same ta idan aka yi la’akari da tashin tashinar da aka shiga a fagen siyasar ƙasar nan kafin zaɓen.
“CUPP na kallon nasarar sake zaɓen Obaseki a karo na biyu a matsayin nasarar da jama’a su ka samu wajen zaɓen irin shugabannin da su ke so ba tare da wata tilastawa ba.”