Zaɓen Edo: Gwamna Wike ya yabi INEC da jami’an tsaro

0

Zaɓen Edo: Gwamna Wike ya yabi INEC da jami’an tsaro

Gwamnan Jihar Ribas, Mista Nyesom Wike, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da hukumomin tsaro kan yadda aka gudanar da zaɓen gwamna na Jihar Edo a ranar Asabar cikin lumana.

Wike ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ke zantawa da ‘yan jarida a Gidan Gwamnati da ke Benin, babban birnin jihar.

Ya ce: “Yanzu ni dai ba ni da ikon bayyana sakamakon zaɓen, to amma daga rahotannin da mu ke samu zuwa yanzu daga wuraren da aka yi zaɓen, ina tsammanin dai mu na farin ciki.

“Ina so in yaba wa INEC zuwa yanzu saboda yadda su ka tabbatar da cewa jama’a sun kaɗa ƙuri’un su a rumfunan zaɓe daban-daban.

“Ina kuma yaba wa hukumomin tsaro zuwa yanzu saboda yadda su ka tabbatar da cewa babu hatsaniya sosai, kuma idan aka ci gaba a haka ina tsammanin wani cigaba ne.

“Shi zaɓe, wani abu ne da ake yi mataki-mataki, ba a kai ga tattaro sakamakon ba tukuna; sai an tattaro sakamakon sannan za mu iya bada ra’ayin mu na ƙarshe.

“Zuwa yanzu dai, zan iya cewa sun yi daidai.

“Abin da mu ke cewa shi ne su tsaya tsayin daka kan abin da ya faru, kuma INEC ta tabbatar da cewa kada wani ya yi ƙoƙarin canza abin da mutane su ka zaɓa wa kan su; abin da mu ke cewa kenan. Idan jam’iyyar APC ce ta lashe zaɓen to a bar shi a haka. Idan kuma PDP ce ta lashe zaɓen, to shi ma a bar shi a haka.

See also  SHARI AR BALA ABU MUSAWA DA MAMUDA LAWAL MAI ZAMANI ALKALI YA TSAME KANSA

“Ina dai jin mun ji daɗin abin da ya wakana yanzu. Ina jin yanzu mu na da rumfunan zaɓe sama da guda 2, 000.

“Ina jin mu na farin ciki sosai kuma idan aka ci gaba a haka wannan zaɓe zai kasance ɗaya daga cikin mafi inganci da za a ce mun gani a Nijeriya.

“Ba wai kawai batun kaɗa ƙuri’a ba ne. Bayan kaɗa ƙuri’a, ana ƙirga ƙuri’u, daga nan sai a tafi haɗa sakamako.

“Wannan shi ne mataki mai matuƙar muhimmanci, kuma lallai ne su tsare cibiyoyin su na tattaro sakamako daga matakin unguwa zuwa matakin ƙaramar hukuma har zuwa matakin jiha saboda duk wanda ya yi zaɓe zai ji daɗin cewa buƙatar sa ta biya.”

A game da labarin da aka riƙa yaɗawa cewa sama da ‘yan sanda 300 sun kai masa farmaki a ɗakin sa na otal a garin Benin a ranar Juma’a, Gwamna Wike ya ce yanzu dai wannan lamari ya zama tarihi.

“Abin da ya faru jiya ya riga ya faru; yanzu kun gan ni, ban bar Edo ba,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here