Ana ƙoƙarin kama matar Dk. Usman Bugaje bisa Zargin Caccakar Gwamnan Kano

0

 

Ana ƙoƙarin kama matar Dk. Usman Bugaje bisa Zargin Caccakar Gwamnan Kano

Barista Sa’ida Sa’ad, matar fitatcen ɗan siyasar nan Dr. Usman Bugaje na fuskantar barazanar kamu daga wasu da ake zargin jami’an tsaron ‘yansanda ne daga Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta turanci ta ruwaito cewa ana neman kama Sa’ida ne bisa zargin caccakar gwamnan Kano, akan yadda ta ce ya ɓarnatar da tallafin Covid 19.
‘Yansandan sun je har garin Kaduna a ƙoƙarisu na kama Barista Sa’ida, wacce take ‘yar rajin kare haƙƙin ce a gidan aurenta, bisa zargin ɓata suna.

A faifan murya da Baristan ta saki, ta yi zargin gwamnan na ƙoƙarin arzuta kan shi da kuɗin tallafin korona.

A halin da ake ciki, ƙungiyoyin sa kai da kare haƙƙoƙin al’umma guda 49 ne suka rattaba hannu a wata takardar ƙorafi tare da kiran jami’an tsaron da su janye daga yunƙurin da suke na kame Baristar.
Ƙungiyoyin sun ce. “A ranar Laraba 16/9/2020, da misalin ƙarfe 5 na yamma, wasu gungun mutane maza da mata suka faɗo gidan Barista Sa’ida Sa’ad dake Kaduna cikin fararen kaya, inda suka yi yunƙurin kamata a zuwan su ‘yansanda ne daga Kano, da aka turo su tafi da ita can Kano, don tuhuma da amsa wasu tambayoyi bisa zargin ɓata sunan gwamnan Kano.”
Sun ƙara da cewa. “Sun zo a motar bas mara tambari da Honda kalar azurfa, inda suka samu jagoranci wata ASP Zainab. Bisa la’akari da matsalar satar mutane da ake fama a ƙasar da kasancewar ba sa ɗauke da takardar sammace, ta ƙi yarda ta fito daga gida, wanda a ƙarshe dole suka tafi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa mutanen sun sake komawa a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 1:15 na rana, ɗauke da takardar sammace.
Jami’an tsaron sun kutsa kansu cikin gidanta, inda suka dinga yi wa ma’aikatan gidan barzana tare da daukar hotunan lambobin motocin dake gidan.

A ƙarshe sun nemi Sa’ida sama ko ƙasa, babu ita a gidan, hakan ya tilasta a wannan karon ma sai tafiya suka yi.

Ƙungiyoyin sun bayyana a shirye Barista Sa’ida take ta amsa sammacen, matuƙar an bi ƙa’idar da ta kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here