Gwamnatin Kano ta fitar da Miliyan 880 din gyaran Makarantu

0

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce tuni ta fitar da naira miliyan 880 domin gyaran makarantun a kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.

Jawabin haka ya fito ne daga mataimakin Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya wakilci gwamna Ganduje, ya  bayyana hakan  a yau lokacin da yake bude taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki dangane da bude makarantu, da ma’aikatar ilimi ta kasa ta shirya da hadin gwiwar  UNICEF.

Taron da hada masu ruwa da tsaki akan harkar ilimi zai tattauna ne game da irin shirye shiryen da akayi dangane da komawa makarantun cikin Yanayin mai kyau tare da samu kariya daga cutar sarkewar numfashi ta Korona.

See also  Over 100,000 persons with Disability receive conditional cash transfer-FG

Mataimakin Gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya ce gwamnarin Kano zata cigaba da feshin magani a makarantun jihar Kano domin Kare dalibai daga kamuwa da cutar Korona.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here