ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (I).

0

Bunƙasar Zazzau da mulkinta sun zo ƙarshe bayan da BareBari suka mulkin Zariya ba tare da yaƙi ba a shekarar 1734. Zariya wanda ta mallake ƙasashen Hausa sai ga ta kwatsam! Ƙarƙashin mulkin Barno.

Daga wannan lokacin sai ta koma kai hare-hare ga Barno a kowace shekara, watau dai sai da ta ɗandana irin mulkin mallakar da ta saba nunawa sauran ƙasashen Hausa.

Da mulkin Zazzau ya koma hannun Barno, sai Shehun Barno ya aiko da wakilansa guda biyu, ɗaya zuwa gidan sarautar Zazzau, ɗaya kuma zuwa ga babbar kotun shari’ar Zazzau. Duk wani abin da zai wakana a waɗannan wurare sai da izinin Shehu. Kowane Sarki idan za a naɗa shi, to wakilan Shehun Magajin Malam shi ke naɗa su. Aikin Magajin Malam ne naɗa sarakunan Zazzau, watau dai shi ne wakilin Shehun Barno mai kula da naɗin Sarauta.

Haka kuma mai kula da sha’anin shari’a a babbar kotun Zazzau mai suna Kacalla, aikinsa ne na tabbatar da duk ayyukan shari’a a kotun Zazzau, Shehun Barno na samun isasshen rahoto. Magajin Malam da Kacalla su ke tabbatar da mulkin Barno a Birnin Zazzau. Haka dai Zariya ta ga wannan mulkin mallakar har ɓullowar jihadin Fulani. A wannan zamani an ce wai rukunin Barebari na da yawa sun shigo lardin Zazzau, da yawa daga cikinsu sun zauna a Zariya.

See also  A DIGITIZED CENTRAL MOTOR REGISTRY FOR THE NIGERIAN POLICE FORCE!

KAFA GARIN BARNAWA

A lokacin da Barno ke mulkin Zariya, watau bayan shekarar 1734, wasu rukunin Barebari ƙarƙashin wani Malami kuma waliyin Allah sun zarto Kudancin Zariya inda suka zauna a rugar Fulanin da ke gabas da Kakuri. Wannan rugar Fulani ta samu shekaru masu yawa da kafuwa kafin zuwan Barebari kamar yadda aka yi bayani a baya.

Za mu ci gaba.

Daga Abdullahi Yahaya Sa’ad.
Head of Admins.
Ƙasar Zazzau a jiya da yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here