DA DUMI-DUMI | Ma’aikatan kotu sun shiga gidan Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa – Hausa7 Nig
A Talatar nan 22 ga watan Satumba 2020 ne ma’aikatan kotu suka cika umurnin alkalin kotun shari’ar musulunci dake Shahuci, malam Garba Kamilu Mai Sikeli, inda suka shiga gidan Malam Aminu Daurawa suka lika masa takardar sammaci.
Idan baku manta ba akwanakin baya mun kawo maku labarin cewa Sheikh Dauda Muhammad Lokon Makera yayi karar Malam Aminu Daurawa a gaban kotu bisa wasu zarge-zarge da yake yi masa akan shirin tambaya mabudin ilimi.
To sai dai kuma tun bayan shigar da kara a gaban kotu, Sheikh Daurawa bai bari an hadu dashi domin a bashi takardar sammaci ba, lamarin da ya sabbaba dage saurarar shari’ar tasu ta ranar 26 ga watan Agusta 2020 da kuma ranar 15 ga wannan watan.
Barrista Ja’afar shine lauyan Sheikh Dauda Lokon Makera, kuma shine ya roki kotu data bada umurnin a shiga gidan malam Daurawa ko kuma duk inda akasan zai ga takardar a lika masa sakamakon bai halarci zaman kotu ba kuma lauyan sa ma bai je ba, inda nan take alkali malam Garba ya amince da bukatar lauyan mai kara yace aje a likawa malam Daurawa takardar sammacin.
Yanzu haka dai ma’aikatan kotu sun likawa malam Aminu Daurawa takardun sammaci a gidan sa da ofishin sa da kuma makarantar sa dake can ‘Yar Akwa a Kano kafin ranar 20 ga watan Oktoba 2020 azo a cigaba da surarar wannan shari’a.
Ga kuma faifan Bidiyon yadda ma’aikatan kotun suka shiga gidan Sheikh Daurawa suka lika masa sammacin. ??