ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (2).

0

ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (2).

Ci gaba.

Shugaban wannan rukuni sunan sa Malam Kilba. Babban Malami ne sosai, cikin hanzari gari ya tashi haikan aka canzama wajen suna zuwa “BARNAWA” saboda bunƙasan sa sanadiyyar zuwan Barebari. Wannan gari ya samu sunan sane daga Barno (wato dai Barno- Barnawa, kamar yadda ake cewa Kano – Kanawa).

Wannan gari tayi tashe sosai, ya zamana Hausawa, Fulani da Barebari suna zuwa neman karatu wurin wannan Malamin.

A lokacin da Shehu Mujaddadi Usman Bin Hodiyo ya bayyana, ance wai ya aiko wa Malam Kilba yana biɗar sa wajen Jihadi. Amma wannan lokacin Malamin ya tsufa sai ya aika masa da manya almajiransa guda biyu a madadin kansa. Sunan Manyan almajiransa Musa Bamalli Da Yamusa. Waɗannan manyan almajira Allah ya ba su haziƙanci da ilmi da fasaha da kwarjini ga kuma ɗimbin karatu.

Ance Malam Bamalli da Malam Yamusa sun bar Barnawa zuwa wajen Shehu Usman Mujaddadi a cikin farkon shekarar 1804. Sun ƙarfi tutar jihadi daga wajensa a wannan shekara, an kuma buƙace su da zuwa Zariya. Malam Musa Bamalli a matsayin Madaki, watau kamar matsayin Sarki, Malam Yamusa kuma a matsayin Madaki. Sun nufo Zariya domin yin Jihadi watau, ɗaukaka kalmar Allah.

Musa da Yamusa sun taho Zariya da askarawan Jihadi ɗari uku da talatin da uku (333), sun auka wa Zariya da yaƙi ranar sati goma ga watan Zul-hajji 1804 A.D. A safiyar wannan rana ce askarawan Shehu suka gwabza da zage-zagi.

Wanda ke sarautar Zazzau a wannan lokacin shi ne Sarkin Zazzau Muhammadu Makau. A wannan ranar Sarki Makau da jama’arsa suna bayan gari wajen Sallar idi. Bayan da aka idar da salla, sai Sarkin ya samu labarin cewa ai Fulani sun mamaye Zariya. Ga shi basu yi shirin yaƙi ba kuma, ba daman su koma cikin Zariya domin ɗauko kayan yaƙi, a hakanan suka gwabza, daga ƙarshe dai Sarki Makau ya gudu, watau dai an ci Zariya ke nan. Sarki Makau ya yi fama da Fulani, amma daga ƙarshe sun sami cimmasa a cikin shekarar 1825 A.D.

Daga Abdullahi Yahaya Sa’ad
Head of Admins
Kasar Zazzau a jiya da yau.

Za mu ci gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here