BA WANDA YA ISA; ALAMAR MI?

0


Daga Danjuma Katsina
Idan ka ji mutum na kirarin ga na tare da shi da magoya baya ko mabiya ko yara ko ma su waye Allah ya hada su; yana jinjina da daga hannun cewa; ba wanda ya isa ya sa ko ya hana shi. Tabbas wannan mutum abin a yi masa tawaye ne; kuma a nuna masa cewa; wannan ba halayyar dan’adam ba ce. Dabi’a ce ta dabbar daji.ko a cikin dabbobin miyagu.
Masu wannan halin suna nuna dabi’a ce ta cewa; su a bariki suka tashi kuma suka rayu. Shi wanda ya taso a gidan girma; an nuna masa ko abokin wasanshi yana iya sa shi kuma ya hana shi.
Masu wannan hali suna nuna; su ba su da kowa, domin mai jama’a shi ne wanda yake aikata aiki kuma yana tafiya ne tare da al’umma; su zamar masa madubi; su riqa kallon shi suna bayyana masa me suka gani. Kuma su qarfafa shi tare da gyarama masa.
Masu wannnan; sun dauko daga cikin manyan dabi’un shaidan; watau girman kai da ji da kai: dagawa da kuma takawa bisa izza a doron qasar da aka yi su da ita kuma za su koma a cikinta
Masu waxannan dabi’u ko da sun yi karatu koma wane iri ne, ko dai ya zama karatun zuqu ko kuma karatun Malam aku. Wanda a fatar baki yake baya a zuci balle kaiwa ga Ruhi.
Masu waxannan dabi’u ba su cancanta su yi mulki ba, domin mulki yana tafiya da shawara ne, da tattaunawa da kuma canza ra’ayi ya tafi daidai da buqatar wadanda ake mulka. In sun samu kansu a mulki bisa makirci ko wani mummunan shiri ko qaddara; masu iya magana ya kamata su buda baki su fada masu, masu rubutu su rubuta, masu fasaha su baje baiwar da Allah ya yi masu.
Sun cancanci,caccaka da fallasa har sai sun gane cewa su ba komai bane.
Allah ka tsare mu da girman kan ba wanda ya isa ya sa mu; ameen.
Danjuma Katsina; mawallafin jaridun Taskar Labarai, The Links News; da Mujjalar Matasa duk da suke a bisa yanar gizo.da kuma mujjalar harshen turanci ta katsina city news mai fitowa lokaci lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here