Makon Kurame: Minista Sadiya ta sha alwashin mara wa naƙasassu baya

0

Makon Kurame: Minista Sadiya ta sha alwashin mara wa naƙasassu baya

Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta ci gaba da mara wa dukkan naƙasassu da kurame baya don a saka su cikin duk wani shiri, a kare haƙƙin su kuma a ba su damar shiga dukkan al’amurran cigaban al’umma.

Hajiya Sadiya ta yi wannan maganar ne a Abuja a ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2020 a wajen bikin zagayowar Makon Kurame na Duniya da kuma Ranar Magana Da Hannu ta Duniya.

Ta ƙara da cewa ma’aikatar ta ta kasance kan-gaba wajen ganin an kafa Hukumar Kula da Naƙasassu ta Ƙasa don tallafa wa muradun dukkan mutanen da ke fama da wata naƙasa a Nijeriya.

Ta ce: “Ɗaya daga cikin dalilan ware Ranar Magana Da Hannu ta Duniya shi ne domin a haɓaka yanayin maganar da kuma al’adun kurame a dukkan faɗin duniya.

“Ina tabbatar maku da cewa Gwamnatin Tarayya, ta hanyar wannan ma’aikata, ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin an kula da dukkan mutane masu wata naƙasa a Nijeriya a harkar gudanar da mulki ta hanyar kawar da duk wani tarnaƙi wanda kafin yanzu ya zame masu ƙargen ƙafa a wajen cigaban su.”

Tun da farko, sai da Sakatare-Janar na Babbar Ƙungiyar Kurame ta Nijeriya, Chidi Topaz Oluije, ya gode wa ministar saboda yadda ta aiwatar da Ranar Kuramen a Nijeriya domin kuwa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce akwai kimanin mutum miliyan goma da ke fama da kurunta a Nijeriya.

Ya ce: “A cewar WHO, akwai kurame miliyan goma a Nijeriya. Wannan ya nuna cewar Magana da Hannu babban muhimmin abu ne a gare mu wajen samun damar cuɗanyar duniyar kurame da ta masu ji tare da shiga cikin harkokin siyasa, kiwon lafiya da duk wani sashe na ƙasar nan.”

Bikin dai ya samo asali ne daga Ƙudiri mai lamba A/RES/72/161 na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda aka rattaba a cikin 2017 kuma aka ware ranar 23 ga Satumba ta kowace shekara a matsayin Ranar Magana da Hannu ta Duniya.

Jigon ranar ta bana dai shi ne ‘Jaddada Haƙƙin Ɗan’adam na Kurame’ (wato a Turance ‘Reaffirming Deaf People’s Human Rights’).

Dukkan masu ruwa da tsaki a wannan al’amari za su ci gaba da ayyukan bikin daga ranar 26 zuwa 30 ga Satumba, 2020 a birnin Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here