Sojojin Operation SAHEL SANITY sun kashe ‘yan bindiga 21, sun rasa Sojoji 3, sun kwato mujallar AK47.
Daga shu’aibu Ibrahim, Gusau
A ci gaba da fatattakar masu aikata laifuka a fadin jihohin Arewa maso Yamma, sojojin Operation SAHEL SANITY sun kashe ‘yan bindiga 21, sun rasa jarumai 3, sun kwato mujallar AK47.
Hakan ya fitone daga bakin mukaddashin Daraktan Daraktan Yada Labarai Birgediya-Janar Bernard Onyeuko a lokacin da yake yiwa manema labaru bayani a faskari , ya ce zaratan sojojin sun yi nasarar fatattakar maharan daga kauyen Unguwar Doka.
Sakamakon samun bayanan sirri sojojin na Operation SAHEL SANITY sun amsa kira cikin sauri kuma ba tare da bata lokaci ba suka garzaya zuwa Yankin inda suka yi nasarar tsarkake kauyen daga maharan.
Sai dai kuma “Abin takaici, sakamakon gamuwa da ‘yan ta’addan, babban hafsan soja da sojoji 2 suka rasa rayukansu wasu sojoji 2 kuma suka ji rauni yayin aikin kuma a yanzu haka suna karbar magani a asibitin sojoji.
An kuma yi kira ga sojojin da kada su Yi kasa a gwuywa kan Wannan aiki sai sun ga an kawar da dukkan masu aikata laifuka a Wannan yanki na shiyyar Arewa maso Yamma, tare kuma da samun tabbacin sadaukarwar sojoji don kare rayuka da dukiyoyin da ke cikin jihohin.
Ya kuma jan hankalin jama’a da su ci gaba da baiwa sojoji bayanai da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan dakile ayyukan masu laifi.