ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (3).

0

ƁULLOWAR BAREBARI LARDIN ZAZZAU DA KAFA GARIN BARNAWA DA SAMUWAR GIDAN MALLAWA DA GIDAN BAREBARI (3).

Ci gaba.

Malam Musa Bamalli sai ya zama Sarkin Zazzau na Farko a mulkin Fulani, shi ne kuma ya kafa gidan Mallawa ( MALLAWA DYNASTY), a sarautar Zazzau. Ya yi sarautar Zazzau cikin 1804-1821.

Bayan rasuwar sarkin Zazzau Malam Musa Bamalli, sai Madakin sa Malam Yamusa ya hau gadon sarautar Zazzau. Shi ne ya kafa gidan Barebari a sarautar Zazzau (BORNO DYNASTY). Shi ma ya yi sarautar Zazzau cikin 1821-1834.
Allahu Akbar! Barnawa babban gari na a wannan lokaci, almajiran Malam Kilba waɗanda sukayi karatu a Barnawa duk sunyi sarautar Zariya wanda ta mallaki makekiyar ƙasa da ƙabilu iri-iri. Irin wannan sabon salon hari na far wa jama’a bayan sallar idi ya sa sauran garuruwa nadama. Ganin yadda aka yi wa sarki Makau, tun daga nan sai ya zamana suna idi a cikin gari ko kuma idan zasu fita sufita da shirin yaƙi.

Garin Barnawa ya cigaba da bunƙasa har zuwan Turawa inda jama’a suka fara fitowa wajen gari suna zama, ta hakane SABUWAR BARNAWA Takafu

Ance wani Malami limami mai suna Malam Rabi’u shi ne ya kafa sabuwar Barnawa. Bakatsine ne, ya fara zama a Kano. A lokacin da Turawa suka ɓullo ya fito waje ya gina masallaci ya haɗa tsangaya ya zauna, a haka a haka mutane nafitowa har gari ya bunƙasa sai aka samai suna SABUWAR BARNAWA.

Lokacin Sarkin Zazzau Ibrahim garin sabuwar Barnawa ta kafu. Ya rasu lokacin Sarkin Zazzau Ja’afaru.

A 1948 sarki Jafaru ɗan Isyaku ya naɗa Muhammad Lawal Sarautar Barnawa.

Wannan shi ne takaitaccen tarihin ɓullar Barebari lardin Zazzau da kafa garin Barnawa da samuwar gidan Mallawa da gidan Barebari.

Daga Abdullahi Yahaya Sa’ad
Head of Admins
Kasar Zazzau a jiya da yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here