Ma’aikatar Kudi na jihar zamfara ta yi karin haske kan kudin wucin gadi.

0

Ma’aikatar Kudi na jihar zamfara ta yi karin haske kan kudin wucin gadi.

Daga Shu’aibu Ibrahim, Gusau

An bayyana cewa Takardun wucin gadi ba kudi ko tsabar kudi ba ne gwamnatin jihar zamfara da gabata ta Karba, ta hanyar wakilcin babban darattan kungiyar gwamnonin Nageriya a madadin jihar zamfara.

Kwamishinan kudi na jihar, zamfara, Alhaji Rabi’u Garba ya sake jaddada haka a ayau a lokacin da yake mayar da martani ga wasu labaran jaridun da ke sukayi amfani da kalmar “kudi” ko “tsabar kudi” wadda gwamnatin Abdul Azizz Yari ce tayi.

Ya bayyana cewa an yi amfani da kalmomin biyu ba daidai ba saboda duk anyi mu’amala ne ta hanyar bincike na wucin gadi.

Da yake bayanin yadda aka tara kudin, kwamishinan kudin ya bayar da kason kudin na wucin gadi da wata mata ma’aikatan kungiyar gwamnonin Najeriya na wancan lokacin suka karba wanda shi ne na farko da ya fara karbar kudin na wucin gadi sama da Naira biliyan 14 cikin gwamnonin.

Kason Kudaden na biyu na wucin gadi sun kai naira Biliyan 22 daga baya DG na kungiyar gwamnonin Nijeriya ya tattara su.

Ya kuma koka kan yadda tattara takardun ya kasance ba tare da cikakkun takardu ba daga gwamnatin mai ci na Gwamna Muhammad Bello, ya kuma bayyana yayin da ya ambaci cewa sanya masu karbar takardun biyu wadanda ba ‘yan asalin jihar ba ne ko kuma ma’aikatan gwamnatin ta Zamfara, ya ce hakan ya saba ka’ida ko muce ka’idoji na aiwatarwa da shimfiɗa ƙa’idodin cibiyoyin kuɗi , Don suna a bayanin sa masu karɓar takardun ba su da alaƙa da jihar zamfara.

A cikin wasikun da suka dace na neman biyan kudin Naira Biliyan N37bn ga duka ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya da kuma Ofishin Kula da Bashin a cewarsa ya bayyana cewa an mayar da kudin ga gwamnatin jihar gaba daya.

Alhaji Garba ya yi zargin cewa mai yiwuwa tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta karkatar da wasu makudan kudade sama da Naira biliyan 10.8 wanda aka tura su kashi biyu, Naira biliyan 5 kowannensu zuwa asusun Jami’ar Jiha.

Ya ce an kuma tura miliyan N850 zuwa wannan asusun a ranar 9 ga Mayu 2019, ya kara da cewa an karkatar da kudin zuwa batutuwan da ba su da alaka da aikin jami’ar.

Kwamishina Garba ya ce an karkatar da jimillar kudin ne zuwa batutuwan da ba su da nasaba da ayyukan jami’ar jihar inda ya tabbatar da cewa gwamnatin da Matawalle ta jagoranta za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta kwato kudaden “domin mu yi amfani da shi wajen ci gaban Jami’ar Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here