Minista Sadiya ta jajanta wa jama’ar Kogi kan fashewar tanka

0

Minista Sadiya ta jajanta wa jama’ar Kogi kan fashewar tanka


Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhinin ta kan lamarin nan na fashewar tankar ɗaukar man fetur wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 20 a unguwar Felele da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Ministar ta ce irin wannan abu ya na ta daɗa faruwa, kuma abin damuwa ne matuƙa, saboda an sha samun fashewar motar ɗaukar fetur ko iskar gas a sassan ƙasar nan a cikin ‘yan watannin nan.

Ta ce: “Na tausaya ƙwarai kuma na damu da aukuwar wannan abu wanda ya ci rayukan mutane da dama waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. Ina yi wa iyalan su da gwamnati da al’ummar Jihar Kogi ta’aziyya a kan faruwar wannan abu. Ina kuma addu’ar samun sauƙi cikin sauri ga waɗanda su ka ji rauni tare da addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda su ka rasu.”

Mai ba ministar shawara kan watsa labarai, Nnneka Ikem Anibeze, ta ce Hajiya Sadiya Umar Farouq ta yi kira da a yi bincike mai zurfi kan wannan abu da ya faru, kuma ta yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki tsauraran matakan kiyaye haɗurra a kan hanyoyi da kuma kare matafiya.

Hukumar Kiyaye Haɗurra a kan Hanyoyi (FRSC) a jihar ta ruwaito cewa mutum 23 ne su ka mutu, ciki har da wani magidanci da matar sa da ‘ya’yan su guda uku, da wasu ɗalibai biyar na Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kogi da kuma ‘yan makaranta. Motoci 10 su ka salwanta a gobarar.

Rahotanni sun ce mutum 10 sun ƙone ƙurmus ta yadda ba za a iya gane su ba yayin da wasu mutum shida su ka samu ƙuna mai ɗan sauƙi.

Fashewar man ta faru ne lokacin da wata mota ƙirar tankar ɗaukar fetur ta ƙwace ta auka wa wata mota safa mai ɗauke da fasinjoji a unguwar Felele.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here