Ba ruwan Minista Sadiya a satar naira biliyan 2.7

0

Ba ruwan Minista Sadiya a satar naira biliyan 2.7, inji ICPC

Hukumar Binciken Ayyukan Cin Hanci Da Rashawa (ICPC) ta bayyana cewa ko kaɗan ba Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ba ce ta ke nufi da saka hannu cikin sace wasu kuɗi na shirin ciyar da ɗalibai a lokacin zaman korona.

A yau ɗin nan ne wasu kafafen yaɗa labarai da mutane a soshiyal midiya su ka baza labarin cewa wai ana zargin Minista Sadiya Umar Farouq da taka rawa wajen sace sama da naira biliyan biyu da miliyan dubu sittin da bakwai (N2.67b) daga cikin kuɗin da aka ware don ciyar da ɗalibai lokacin da ake zaman dirshan saboda annobar korona.

Hakan ya biyo bayan jawabin da shugaban hukumar, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya yi a jiya Litinin, 28 ga Satumba, 2020 a wajen Babban Taro na Ƙasa kan Raguwar Cin Hanci da Rashawa, karo na biyu, a Abuja.

Hukumar ICPC ta ce rahotannin sun tafka kuskuren cewa Hajiya Sadiya ce ta kautar da kuɗin na shirin da ake kira “Home-Grown School Feeding Programme”.

Abin da Farfesa Owasanoye ya faɗa a jawabin sa a taron, shi ne, “… mun gano cewa wasu kuɗaɗen da aka biya ga wasu kwalejojin gwamnatin tarayya (makarantun sakandare) don ciyar da ɗalibai ‘yan sakandare, wanda sun kai N2.67 biliyan lokacin zaman dole a sa’ilin da ‘yan makaranta ba su zuwa makaranta, sun shige aljifan mutane ne.

“Mun soma bincike kan waɗannan abubuwan da mu ka gano.”

Hukumar ta ce ta na so ta faɗakar da jama’a cewa “ciyarwar ‘yan makaranta” da shugaban ICPC ya ambata ita ce ta ɗalibai da ke kwana a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya, waɗanda duk su na zaune a gida a lokacin zaman dole na annobar COVID-19.

Ta ce: “Wannan BA shirin ‘Home-Grown School Feeding Programme’ ba ne wanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya.

“Hukumar ta gano a lokacin da ta ke nazari kan takardun Gidan Yanar Buɗaɗɗen Asusu (Open Treasury Portal) cewa kuɗaɗen da aka kasafta za a riƙa kashewa a wata-wata kan ciyar da ɗaliban makarantun sakandare na WASU daga cikin Kwalejojin Gwamnatin Tarayya ana kautar da su zuwa asusun wasu mutane.

“Mun fitar da wannan sanarwar ne domin mu yi ƙarin haske kan bayanin da Shugaba ya yi.

“Saboda haka, mu na sanar da dukkan jama’a cewa su yi watsi da waɗancan rahotannin da su ke cewa shirin ciyar da ɗaliban makarantun firamare ne mu ka yi magana a kai.”

Hukumar ta faɗa wa duk mai buƙata cewa zai iya sauko da cikakken jawabin da shugaban ya yi daga gidan yanar hukumar da ke intanet a wannan adireshin, wato www.icpc.gov.ng.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here