WAKAR BULALIYA TARE DA MALAM SANI YUSUF AYAGI

0
360

WAKAR BULALIYA TARE DA MALAM SANI YUSUF AYAGI

Randa duk kwana ya kare
ko a daki ko a zaure
ka rufe kofa da kyaure
zata zo RAN za a zare ba da kai mata ja inja ba

Ba a jinkirtama kowa
ba a gaggautama kowa
ajami ko larabawa
in ta zo ko sai macewa ko sakan ba a dadawa

kunji dai ku ‘yan uwana
manya manya da kankana
zata zo musu ko a gona
ko a daki ne na kwana In ta zo baza su kwan ba

Malamai ko jahilawa
masu kudi talakawa
masu mulki dogarawa
zata zo musu ba rabewa ba ganin matsayi take ba

Dubi ayar kur’ani
kullu nafsin tai bayani
za’iqatul mautu aini
ko a kauye ko a birni babu wanda ba zai mace ba

duk mutum da sanadinshi
wani yai cuta ta jashi
wani ba ciwo ta kaishi
wani ko hadari silarshi babu yadda bazata zo ba

wani na yawo a titi
wani na ciniki a kanti
wani ko na shafa fenti
wani ko ya kama kati bai sani yau zai mace ba

wani na fama da aiki
wani na sukuwa da doki
wani na wanka a tafki
wani ko ya kama wanki zata zo bai karasa ba

wani ko na cin abinci
wani ko sai yayi barci
wani na fama da kunci
wani ko a cikin takaici zai mace bai ma sani ba

wata na tukin tuwanta
wata tazo haihuwarta
wata ko na kan gadonta
zata zo dan zare ranta bada ta farka anan ba

mutuwa ita ba ruwanta
inta zo ba mai hanata
babu mai ikon tareta
masu mulki ko wadata dai cikinsu bazai hana ba

ba ruwan mutuwa da mulki
Ba ruwan mutuwa da mulki
ko na mai rawaninga sarki
in ta zo tilas ta dauki ransu mulkin bai hana ba

dubi jariri kamar shi
sai yana hannun uwarshi
ta riga ta rungumeshi
sai ta rabo tsaf ta jashi ga uwar bata ko hana ba

ko ta dauki uwar ta barshi
ba ruwanta da tausayinshi
bata duban wai uwarshi
zata dau nono ta bashi inta zo ba za ya sha ba

Mutuwa bata kulawa
saurayi ko ‘ya budurwa
yanzu ta maishe su gawa
babu sauran shakatawa bako zata jira biki ba

Mutuwa ba raya shaho
ta buge yaro da tsoho
ta kade kuturu makaho
wani ma tun kan a haihu zai mace ko ba da wai ba

Mutuwa inhar ta sauka
a gida wani zata dauka
ba ruwanta da masu sanka
yanzu kaji ana ta kuka wanda bai hana dauke ran ba

yanzu aya zan karanta
‘yan uwa kowa ya jita
ko wani zaiga ma’anarta
yadda kowa zai kowa fahimta ba tare da na barta a dunkule ba

Aina ma kuntum ku gane
yata rukumul mautu kune
ai walau kuntum mutane i burujun can gaban ne ‘yan uwa ban karasa ba

Ma’ana Allahu yace
ko ina ne kun kasance
zata zo muku karku mance
Mutuwa Ala-sa mu dace kan ta zo mana duk mu tuba

kunji dai zance na aya
gaskiya ce babu karya
ko ina ne kunka buya
zata zo muku sai ku shirya ba shirin shan magani ba

Ga misali mai kulawa
Mursalai haka annabawa
ga sahabu da auliyawa
sun wafati da dadewa in kana ji ne da kanka

da isa ko dukiyarka
ko yawan mulki gareka
can a baya akwai gabanka ya wuce bai dakata ba

In yawan bauta gareka
rabbi yai wani kan ayika
wanda in bautar yafika
daukakar ya sha gabanka ya wuce bai ko tsaya ba

Kunji tarihi da kissa
Annabin Allah da kansa
wanda babu mutum kamarsa
Musdafa an zare ransa ya waninsa ba zai mace ba

wanda zabi anka bashi
shin a dau ran ko a barshi
Daha dan jarumtakarshi
sai ya zabi a zare ranshi bai bukaci ya dakata ba

Dan uwa bar shirya fati
kyale cin naman faranti
tunda annabi yai wafati
babu mai ikon sabati duniyar nan bai mace ba

Da uwa da uba gareni
sai uban ya mace ya barni
tun ina karami ku ganni
sai uwata ta rikeni har na girma ba zan rufe ba

Sai na girma gaban uwata
sai ta kyautata rayuwata
har ta min aure da kanta
gashi yau ni na rasata ban ko samu kamarta dai ba

Duniyarnan ba kamarta
shi yasa in na tuno ta
yadda tai mini tarbiyyarta
sai nace Allah jikanta . . .

Gashi yau na samu kaina
ba uwata ba ubana
sun bacewa ganin idona
to ashe wataran kwa raina zai bace ko ba da wai ba

‘Yan uwa in kun fahimta
duniyar da muke cikinta
dole kowa zaya barta
babu mai ikon suturta wai yace ba za ya kau ba

‘dan uwa bari yin dagawa
dan ganin ka samu baiwa
bar ganin ka zarce kowa
mutuwa na kewa yawa babu inda bazata je ba

Ran da duk aka zare ranka
yan uwanka suna ta kuka
wanda bai dawo da ranka
ai su ce Allah jikanka zaji ba sui ta kururwa ba

Burinsu kawai a kaika
a saka ka a kabarinka
sai su zo kan dukiyarka
sui rabo ba mai tuno ka sai kace basu sanka da ba

da kana mulkin gidanka
yanzu bamai girmamaka
babu sauran bada doka
babu mata ‘ya’ya da jika sai kace basu sanka dai ba

Alhajin Allah kamarka
mai isa da isa ya sanka
gashi yau likkafaninka
ba a sa shadda a dinka sai farin alawayyo duba

kaga tarin dukiyarka
bata amfani gareka
duk yawan motar gidanka
ba a kaika a marsidinka sai kace ba taka ce ba

‘dan uwa kardai ka mance
duk kudin nan naka nace
anyima gata fitaacce
sai a dau motar itace a saka ba marsidinba

matukar sun girmamaka
sug gine kabaringa naka
daga nan sun sallameka
ko ziyara in gayama sai su shekara ba su jeba

Dubi duk girman gidanka
sai ya zam kango rashinka
wanda ba ya shiga da ranka
sai ya aure sahibarka yash shige ba a mar hani ba

Dan uwa in an saka ka
a cikin kabaringa naka
ko ina an toshe iska
babu mai sha’awar taya ka shi zaman nan ba da wai ba

Sai a tashi kawai a barka
daga kai sai dai halinka
sai mankir nankir su sauka
sush shigo dan tambayarka duk da ko baka san guda ba

Sai a dawo ma da ranka
sai su hau bisa tambayarka
in ka amsa sai su barka
sai a yalawata kabarinka ba a barshi a takure ba

Inko har suka tambayeka
babu amsa zaka koka
sai su hauka kawai da duka
sai a matsatse kabarinka har gabobi duk su bamban

Sai a nuna ma makoma
hawuya koko jahima
inda nan zakai ta fama
har zuwa tashin kiyama babu sassaucin azaba

‘Dan uwa zan sake janka
kar ka ce na tsorata ka
zanyi ma zancen gidanka
inda farko za a kaika sanda ka mutu ba da wai ba

Kwanciyar kabari tuno ta
ba katifa zaka yi ta
ba filo haka zaka kwanta
babu juyi dan ka huta kaji ba karya nake ba

Babu haske babu iska
babu ac babu fanka
kai ka dai ba sahibarka
sai abinda kawai ka aika zai fito maka ba da wai ba

Kwanciyar nan ko a barka
babu zagi babu duka
kaita bacci dai abinka
wata ran ka so ka fark bada an maka izini ba

To bare kuma babu tashi
ga gumi zafi ka sanshi
ba rigingine sam cikinshi
ya ka shirya zaka yi shi baka sa Allah gaba ba

Kaji dai yana yin cikin shi
gashi ya zama babu fashi
dole kowa zai shi ge shi
ya kamata ka tanajeshi da yawan zikiri da tuba

In gaya muku ‘yan uwana
kun sakankance ganina
sai yawan sabo da barna
sun sani da wuta da jannah ya ba mu yi musu tana di ba

Shugaba kake ko ko gwamna
ofishin nan naka auna
wanda kai ka shige ka zauna
sai ka dau biro ka zana kai zaton fa ba’a sani ba

In tuna maka karka manta
karka yarda ka shirya cuta
ko kadan ce karka yita
in ko kayi an rubuta bako gogewa ake ba

Karka ce ba’a ganinka
tunda ba’a shiga wajenka
sai da yin izini a ganka
to kaji Allah na ganinka ga rakib da atib ka lura

duk abinda kake ka gane
shin na kirki ko tsiya ne
su suna hangenka zaune
sun rubuta ko kadan ne basu kyale ko guda ba

‘Dan uwa komai ka shuka
zai fito kaji babu shakka
zaka girba kai da kanka
Randa ka mutu kai da kanka zaka zana ba da wai ba

Sun ka ce can nayi sata
can ko na bai wane kyauta
can ko naci hakkin makota
kayi alheri da cuta baka biye ko guda ba

shin ku dubi mu’amalarmu
mun sake sam ba ruwanmu
bamu tanyon ‘yan uwanmu
dukiya daga mu diyanmu bamu ba kowa kwabo ba

kasuwarmu Idan ka duba
bamu ware haram halal ba
bamu san zi da ribaa ba
bamu bar yin algushu ba sai kace ba zamu kau ba

‘Yan uwa tuni ni na lura
mun sakankance da naira
burikanmu kawai mu tara
ba tunanin zamu saura bamu dau mutuwa akwam ba

Ga shigarta kwarai ganina
gashi mun cika cin amana
ga yawan sabo da barna
sabuka manya kanana yi muke karya da giba

Ni abinda ka bani haushi
‘dan adam sam ba ruwanshi
bai kula da abin gaban shi
ko hisabin dukiyarshi dan uwana bai kula ba

Wanga wake ‘yan uwana
nayi dan wa’azi akaina
dan na lura na gyara kaina
in rage sab’o da kaina in tuno mutuwa na tuba

Dan ganin ni na shagalta
mutuwa bana tuno ta
ban tunanin ya kamarta
nafi kyautata duniya ta lahira ban ko kula ba

Shi ya sani na wallafa ta
dan tunawa zuciyata
da akwai mutuwa gabanta
ko da yaushe zata zo ta bakwa sa rana take ba

Nafi so naga na wadata
na sayo babur da mota
marsidis honda tiyota
ga gidana har da kwalta can a gefe ba gari ba

In yi dinkin kece raini
riguna ko wanne launi
shadda boyal na aini
nayi dan nima a sanni mai kudi ne ba kadan ba

Nan da nan kaga nai abokai
masu kuddi har sarakai
masu mulki malamai sai
sui ta dan kamin mukami duk da ban iya godiya ba

Sai a ce an ban sarauta
shugaban duka masu kyauta
aita famar gayyata ta
gun afil fand nai ta kyauta ba ‘yar kadan ba

Malamai ko su zo gidana
sui ta nemana mu gana
sai a ce musu nayi kwana
sai su sami guri su zauna basu san ko zan fito ba

Sai su kirkiri yin karatu
ko su kawo min rubutu
wai na sha dan kar na zautu
dukiya haka sai da hutu kai magauta suc ci riba

gun biki sai an jira ni
duk ana burin a ganni
in nazo fa a kewayeni
ga maroka na zugani inyi kyauta ba kadan ba

To a sannan na gama ni
dole kowa zaya bini
yaita famar girmamani
sai ace komai sai an jirani ko abin ni ban sani ba

dukiya ta ja sarauta
na zamo malam akanta
ba a karyata magana ta
sai a so ni maza da mata duk da ko ban san alif ba

ba a karyata magana ta
ko a yaya ni nayi ta
ko nace na shuka fata
ta fito kuma naga dan ta wani zai ce ba da wai ba

Ana haka sai na gane
duniya wani gun zama ne
burinka da nake haram ne
mai nutsar da mutum a zaune wanda bai dace da ni ba

Mutuwa ni bani san ta
bani san naji ambatonta
dan tana kada zuciya ta
take sai kaga na dimauta kwarjinin fa ba zai gushe ba

Na sani ita gaskiya ce
naji lallai na amince
zata zo ba kauce-kauce
to fa Allah na dimauce dan kwa ban mata tanadi ba

Mai ya sani nake gudunta
yadda malam ya fade ta
gashi yadda ya suffata ta
naga babu gwani a gunta yaya ba zan fargaba ba

Ba macewar nag guda ba
mutuwa ni ba da wai ba
ba ina kyamarta ne ba
karta dau raina ku duba kwanciyar kabari na duba

Nayi sab’o ba kadan ba
gashi ba sadaka nake ba
ni ko ban wata nafila ba
ban yi aiki masu kyauba ya ba zan mata farga ba ai

Ni mutum ne mai kasala
mai bukatar tara daula
gani bana san wahala
banda sallolin farilla gashi ban wani tanadi ba

Inka duba ayyukana
wanda dai ni nai da kaina
manya manyan laifukana
nai nadama ni da kaina rabbi ba zan sake yi ba

In na dubi abinda nay yi
laifuka ne masu nauyi
sai jikina yay yi sanyi
sai kawai rokon buwayi gafara ba sake yi ba

Tunda yanzu idan ka ganni
duk gabobi sunyi rauni
ya gwani ar-Rahamani
Nayi rokona da nuni kaj ji kan ummi da abba

Rabbi wanke mahaifiyata
dagga dukan laifukanta
dole nai roko ka sata
can gidan rahama ta huta ba da an mata bincike ba

Rabbi kaine Arrahimu
Shafe dukkan laifukanmu
duk abinda mukai ka barmu
a gidan nai’mu ba da ka kula laifukanmu

Rabbi baban ka barshi
kar a bincika ayyukanshi
naay yi roko jalla sashi
cancikin firdausi sashi rahama bai sha wuya ba

Duk hakkina ya biyani
ya gwada mini kur’ani
makaranta shi ya kaini
yayi min horo da nuni bai gwadan san zuciya ba

Ya gwani Allah karimi
zul-jalal wal’ikirami
nayi roko ya rahimi
kaj jikan dukkan musulmi hada kanmu mu daina gaba

Naga nan ne ya kamata
‘yan uwana in takaita
in batun mutuwa na huta
Allah sa dai mun fahimta ba mu barta mu shantake ba

Wanda duk ya tsaya ya jita
ko ya dauka ya karanta
inda yagga kure cikinta
Yai yi himma dan ya gyatta sani bai wuce yin kure ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here