Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya amince da a bude makarantu a jihar, inda za a buɗe su daga ranar 11 ga watan Oktoba.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sunusi Muhammad Kiru ne ya bayyana haka yau a kano,
Kwamishinan ya ce ‘yan aji shida da aji biyar na firamare za su koma makaranata a ranar 11 ga watan Oktoban 2020.
Yayin da ‘Yan aji ɗaya da biyu kuma za su rinƙa zuwa makaranta a ranakun Litinin da Talata kawai, inda za su fara daga 12 ga watan Oktoba.
Sai kuma ‘yan aji uku da huɗu da biyar na makarantun firamare su ma za su rinƙa zuwa Laraba da Alhamis da Juma’a inda za su koma ranar 12 ga watan Oktoba.