Kungiya mai zaman kanta ta bukaci a aiwatar da rahoton sufeto janar a zamfara

0

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Wata kungiya mai zaman kanta Muryar Zamfara ( Voice of zamfara) a turance ta yi kira ga gwamnatin jihar ta Zamfara da ta gaggauta aiwatar da rahoton da kwamitin da ta binciki masu sabbaba kisan mutane da sacesu karkashin jagorancin tsohon Sufeto Janar na‘ yan sanda (IGP) Mohammed Abubakar don kawo karshen ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara.

Shugaban kungiyar mai zaman kanta Muryar Zamfara ( Voice of zamfara) a turance , Salisu Muhammad Moriki ya yi wannan kiran a yayin ganawa da manema labarai a Gusau bayan taron kungiyar karo na biyu.

Moriki ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta kafa kwamiti karkashin jagorancin tsohon shugaban IGP Mohammed Abubakar’ wanda ya jagoranci kwamitin don binciko musabbabin rashin tsaro da nemo mafita mai dorewa ga ‘yan fashi a jihar.

Ya ce “Muryar Zamfara na kira ga gwamnatin jihar, cikin gaggawa, don aiwatar da shawarwarin da kwamitin kwararru ta bayar domin samun dawwamammen mafita ga matsalolin tsaro da ke fuskantar jiharmu ” in ji shi.

See also  Majalisar Kogi Ta Bada Umarnin Kulle Kamfanin Simintin Obajana, Mallakar Ɗangote

Shugaban ya kuma jinjinwa gwamnati da hukumomin tsaro bisa jajircewa da kokarin da suke yi na magance matsalar rashin tsaro a fadin jihar

Moriki ya bayyana bacin ransu tare da Allah wadai da zanga-zangar da kungiyar da aka fi sani da Coalition for Northern Group (CNG) suka shirya kwanakin baya a jihar wacce ta bukaci kame wasu ‘yan siyasa a jihar.

Muhammad ya bayyana kungiyar masu zanga zangar a matsayin kungiyar haya, da wasu ‘yan siyasa suka shigo da su cikin jihar domin siyasantar da Wannan matsala ta rashin tsaro dake addabar jihar.

“Mun yi tir da duk wani yunkuri na sanya batun tsaro a cikin harkar siyasa a jihar mu, kuma bamason duk wani yunkuri na lalata zaman lafiyar da muke da shi a halin yanzu , ”inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here