Haƙiƙa an sha dambarwar a Najeriya, tun daga samun ‘yancin kanta, har izuwa yau, waɗanda za mu iya cewa su ne ƙashin baya wajen hana ƙasar cigaba.
Najeriya ƙasa ce mai al’adu da addinai da ma ƙabilu daban-daban da suka haura 200. Manya daga cikinsu, su ne, Hausa da Ibo da kuma Yoruba, wanda kowannen su yana da tsarin yadda yake tafiyar da mulkin jama’arsa.
Bayan da aka raba ƙasar zuwa yankuna uku, wato Hausa da Fulani (da sauran ƙabilun su) a yankin Arewa, Ibo (da sauran ƙabilun su) a yankin Gabashi, Yarabawa kuma a yankin Yamma, Arewa ta fi kowanne yankin yawa da kuma girma, abin da sauran yankunan suka yi ta kokawa a kai.
A shekarar 1940 zuwa 1950, jam’iyyun da aka kafa domin yaƙin kwatarwa Najeriya ‘yancin kai, su ne, NPC (Northern People’s Congress) a Arewa, NCNC (Nigerian National Democratic Party) ta ƙabilar Ibo, da kuma AG (Action Group) ta Yarabawa. Waɗannan jam’iyyun sun yi ta gwagwarmaya musamman NCNC da AG waɗanda ke neman a ba su ‘yancin cin gashin kai, abin da suka ga zai yi wuya, ba tare da sun haɗa kai da Arewa ba.
Hakan yasa jam’iyyun uku suka haɗu suka yi ta gwagwarmayar tare.
Sir. James Willson Robertson, shi ne Gwamna Janar na ƙarshe a tarihin mulkin mallaka a Najeriya. Ya soma mulki a ranar 15 ga watan Yunin 1955, sannan ya miƙa mulki a hannun Dr. Nnamdi Azikwe, wanda shi ne baƙar fata na farko ɗan Najeriya da ya fara mulkin ƙasar, a ranar 16 ga watan Nuwamban 1960.
Zan cigaba.
Muhammad Bala Garba.
2 ga watan Oktoban 2020.⅝55⅝66