@ jaridar taskar labarai
Mai ba gwamnan katsina shawara a harkar noma ya shaida wa taron manema labarai cewa, Hari akan manoma Wanda miyagu masu dauke da makamai ke kaiwa.ya Sanya a daminar bana an kasa noma gonaki guda dari biyar a duk fadin jahar kamar yadda binciken su ya tabbatar masu.
Yace fadin yawan wadannan gonakin sukai yawan hekta dubu hamsin da takwas,
Mai bada shawarar yace wannan ya Sanya yawan abincin da jahar ke samu zai ragu da kashi talatin cikin dari .
Mai bada shawarar ya kara da cewa bincike ya tabbatar masu da cewa cutar Coronavirus bata shafi matsalar noma ba, amma dai ta shafi daukar abinci daga nan zuwa can.
Mai bada shawarar yana jawabi ne a taron mako mako da ma aikatu da hukumomi ke yi ga manema labarai akan cigaban da hukuma ko ma aikata ta samu a zamanin mulkin wannan gwamnatin.
Mai bada shawarar ya kuma bada bayanin cewa matsalar cutar covid 19 ta haifar da rashin ba manoma takin noma a wannan shekarar. Ya kuma ce kowane buhun takin gwamnati na sayen shi akan kudi Sama da naira dubu bakwai.amma gwamnati takan saukaka farashin,
Mai bada shawarar Alhaji abba yusufu yace sun fito da tsari na bada taki Wanda ke isa kai tsaye ga talakkawa ba kamar yadda ake ada ba.wanda sai wane da wane ke samu.
Mai bada shawarar yace , sun tsara inganta bukin noma na shekara shekara wanda za a rikayi a garin kafin soli don karfafa wa manoma.yace za a kewaye filin da Bango don inganta wannan buki .
Mai bada shawarar yace, jahar zata kara inganta harkar noman rani da tallafawa manoman don basu karfin gwaiwa da habaka harkar.