Shugaba Trump da Matarsa sun kamu da cutar Konona

0

Daga Ibrahim Hamisu

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kamu da cutar sarkewar numfashi ta Korona, wato COVID 19, kwanaki 31 kenan kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar.

Trump ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko.

Ya ce “A daren yau, ni da “FLOTUS mun kamu da COVID 19. Za mu killace kanmu ba tare da bata lokaci ba

Za mu ci galaba a kan wannan tare!” kamar yadda ya rubuta.

A kwanakin baya dai an ruwaito Shugaba Trump yana sukar yadda ake neman siyasantar da batun cutar korona zuwa ga wani abu na daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here