HARIN DA AKA KAI FASKARI DA SABUWA A YAN KWANAKIN NAN
Muazu hassan
A ranar 27/9/ 2020 yan ta adda sun je mai garin mai gangumma sun harbi mutane uku sun kuma dauki mutane Goma sha daya.kamar yadda wakilan mu suka tabbatar,,garin mai ganguma suna a cikin karamar hukumar faskari
A kuma ranar 3/10/2020 garin dungun muazu a wata unguwa mai suna kabalawar dungun muazu sun harbi mutum biyu , daya ana tsammanin ya mutu. Sun dauki mutum biyu mata da miji.
A ranar 30/9/2020 wadannan maharan sunje garin damari hayin kasuwa inda suka tafi da mutane Goma har da wata mata da goyon dan ta.damari na cikin karamar hukumar sabuwa.
har zuwa rubuta rahoton nan ana magana da yan bindigar don su sako su.amma ba cimma matsaya ba.
@ jaridar taskar labarai. Www.taskarlabarai.com
@ Katsina city news .www.katsinacitynews.com