HARIN ‘YAN BINDIGA A TSAUWA, GASKIYAR ABIN DA YA FARU

0

HARIN ‘YAN BINDIGA A TSAUWA, GASKIYAR ABIN DA YA FARUFARU

.
@ jaridar taskar labarai ( binciken da mukayi)
A ranar juma’a 02-10-2020 da rana tsaka misalin 1:00pm wasu mahara dake kan babura suka tarbe wani mazaunin kauyen Tsauwa mai suna Ayada. Mai sana’ar Kabu kabu da babur, lokacin da yake dawowo daga kauyen Mazanya inda yakai wata mata.
Maharan su hudu kowanensu dauke da bindigar bature ta AK47,suka bukaci ya basu babur dinshi. Bayan sun kwace masa babur, kuma sai sukayi kokarin tafiya da shi da nufin yin garkuwa da shi. Amma sai ya tsallake ya gudu daga bisani kuma ya kira ‘yan garin su (Tsauwa) ya bayyana masu abin da ke faruwa domin su kawo masa dauki. Bayan sunyi nasarar haduwa da shi, akan hanyarsu ta komawa gida gab da fita kauyen Yauyau daidai masussukin kauyen ‘yan bindigan sukayi masu kwanton bauna suka bude masu wuta.
Inda nan take suka kashe masu mutane biyar daga nan sai suka kama harbe harbe, tsakaninsu da maharan dayake suna dauke da ‘yan bindigogin su na toka (harba ruga), ana cikin wannan dauki ba dadi sai jirgin jami’an tsaro yazo yayita shawagi yana zagayawa su daga bisani kuma ya tafi.
Bayan kura ta lafa an kara samun gawawwakin mutanen Tsauwa hudu wanda ya bada jimillar mutune tara (9) suka rasa rayukansu a wannan artabu da akayi.
Jama’ar kauyen da muka zanta dasu sun koka kan kin kawo masu dauki daga jami’an tsaro cikin lokaci.koda yake zuwan jirgin sama ya tsorata maharan.ganin yadda lamarin ya faru da rana kata amma basu ga keyar kowa ba Saida aka gama kashe masu mutane su kuma maharan sun sukale sannan aka kawo masu motocin jami’an tsaro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here