Za a sake tantance masu cin moriyar shirin N-Power da aka tsallake wajen biya
Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta umurci masu cin moriyar shirin tallafi na N-Power, rukuni na ‘A’ da na ‘B’, waɗanda aka tsallake sunayen su wajen biyan kuɗi a watannin baya da su hanzarta zuwa ofisoshin jami’an shirin na jihohin su don a sake tantance su.
Wannan umurnin ya fito ne daga wajen Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, a ƙoƙarin da ta ke yi na warware cikas ɗin da aka samu na rashin biyan wasu masu cin moriyar shirin saboda matsalar da aka samu wajen tantance bayanan su, wanda yanzu an kusa kammala warware matsalar.
Binciken da ofishin Akanta-Janar na Tarayya (AGF) ya kammala lokacin da aka tsallake sunayen waɗansu masu cin gajiyar shirin na N-Power ya gano cewa wasu daga cikin masu cin gajiyar shirin su na kuma karɓar kuɗi daga sauran ma’aikatu ko hukumomin Gwamnatin Tarayya.
To sai ministar ta bada umurnin cewa a ba waɗanda abin ya shafa dama su sake miƙa takardun su domin a ga ko sun cancanci a biya su kuɗin shirin na N-Power.
Saboda haka ne ministar ta yi kira ga masu cin moriyar shirin da su je ofisoshin jami’an shirin a jihohin su ba tare da ɓata lokaci ba don su bada bayanan asusun su na banki da takardar hidimar kuɗi (statement) na akawun ɗin asusun daga watan Maris 2020 zuwa yau, da takardar shaidar gama bautar ƙasa (NYSC) da sauran takardun da ake buƙata.
Mai hidimta wa ministar kan aikin jarida, Nneka Ikem Anibeze, ta faɗa a wata sanarwa cewa an ƙayyade 13 ga Oktoba, 2020 a matsayin ranar da za a rufe tantancewar.
Ta ce duk wani mai cin moriyar shirin wanda ya gaza zuwa tantancewar ba za a biya shi kuɗin ba.