JAMI’AN KWASTAM SUN CAFKE WANI DA KATUNAN ATM FIYE DA 5,000 A KANO

0

 

Daga Ibrahim Hamisu, Kano

Jami’an hukumar Kwastam ta jihar Kano sun cafke wani mutum dauke da katunan ATM fiye da 5,000

Hukumar yaki da fasa kauri ta ƙasa shiyyar Kano da Jigawa ta samu nasarar damƙe wani matafiyi ɗauke da katunan cirar kuɗi wato ATM kimanin guda 5,342, a filin tashi da saukar jirgin sama na Malam Aminu Kano.

Shugaban shiyya na hukumar Nasir Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke miƙa wanda aka damƙe din ga jami’an hukumar hana yi wa tattalin arziki ta ƙasa ta’annati wato EFCC.

Nasir Ahmed ya ce sun kama mutumin ne a lokacin da ya ke kokarin tafiya ƙasar Dubai, inda su ka gan shi da wasu buhunan wake guda 2 cike da katunan na ATM.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here