Daga Ibrahim Hamisu, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da ranar 26 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a sake buɗe manyan makarantun gaba da sakandire a fadin jihar.
Hakan ya fito ne daga Kwamishiniyar Ilimi mai zurfi ta jihar Kano, Dakta Mariya Bunkure a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai a ofishinta, ciki harda wakilin Jaridar Taskar Labarai na Kano.